Islamic Chemist

Amfani 9 na bawon ayaba ga lafiyar Dan Adam

Amfani 9 na bawon ayaba ga lafiyar Dan Adam:

Amfani 9 na bawon ayaba ga lafiyar Dan Adam:

Bawon ayaba yana kunshe da arziki na sunadaran gina jiki (nutrients) da kuma masu sanya karfin jiki (carbohydrates). Akwai ire-iren sunadaran vitamin B6, vitamin B12, magnesium da kuma Potassium wadanda suke da alfanu daban-daban ga lafiyar jikin dan Adam.

Ga jerin hanyoyi 10 da bawon ayaba ke inganta lafiyar jikin dan Adam.

1. Hasken hakori:

Goga bawon ayaba ga hakora sau daya a kullum har na tsawon sati guda ko da kuwa na minti guda ne, yana matukar kalkale hakora su fita tar kamar haksen walkiya.

2. Fitar da tusar jaki:

Mulka bawon ayaba yana taimakawa wajen ficewar tusar jaki da kuma hana bayyanar wat sabuwa a jikin dan Adam

3. A matsayin ci ma:

Ana amfani da bawon ayaba a matsayin abin ci, domin kuwa mutanen kasar Indiya sun gano cewar sanyawa dahuwar kaza bawon ayaba yana kara laushin tsokar ta kaza.

4. Waraka ga kurajen fuska:

Goga bawon ayaba ga kurajen fuska cikin minti 5 har na tsawon mako guda za a sha mamaki.

5. Rage yakunewar fata:

Hada bawon ayaba tare da kwanduwar kwai kuma a shafa ga fuska sannan a wanke da ruwa, ya na matukar warware fata ta yi luwai-luwai.

6. Sauki ga bugewa a jiki:

Shafa bawon ayaba ga wata buguwa ko wani ciwo na jiki yana taimakawa wajen rage radadin ciwon cikin gaggawa.

7. Waraka ga cutar makero:

Bawon ayaba ya na taimakawa wajen kawar da cutar makero wadda turawa suke kiranta da Psoriasis. Ya na kuma taimakawa wajen rage radadin kaikayi na makeron

8. Cizon kwaruka:

Shafa bawon ayaba akan cizo kamar na sauro yana dauke kaikayin zafin cizon

9. Kyalkyali

Goga bawon ayaba ga fatar takalmi, jakar leda ko azurfa yana sanya su zamto cikin kyalkyali a koda yaushe

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button