LABARAI/NEWS

An aike da mutumin da aka kama da katinan zaɓe 29 zuwa gidan yari a Kano

An aike da mutumin da aka kama da katinan zaɓe 29 zuwa gidan yari a Kano

Wata kotun majistare a Kano ta tasa keyar wani matashi zuwa gidan yari har sai an yanke hukunci kan neman belinsa

A kwanakin baya ne yan sanda su ka kama Wani mai shekaru 45 da katinan zabe na dindindin guda 29 mallakar wasu al’umma a karamar hukumar Dawakintofa ta jihar Kano

Don haka lauyansa ya mika bukatar neman belinsa amma mai gabatar da kara ya ki amincewa da bukatar

Daga nan ne Alkalin Kotun ya dage ci gaba da sauraron karar zuwa karshen Janairu domin yanke hukunci kan neman belin wanda ake zargin

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button