LABARAI/NEWS

An cafke Dan ta’addane tare da Harsasai a Hanyar Jos Zuwa Dandume Jihar Katsina

An cafke Dan ta’addane tare da Harsasai a Hanyar Jos Zuwa Dandume Jihar Katsina

Wakilinmu ya Shaida Mana yadda Akayi Nasarar cafke wannan mutumin a Daren Jiya Lahadi 25/09/2022, “inda ya hau wata mota kirar Sharon

A Cewar shi ya Shiga motarne daga tashar farar gada, inda ya nufo ta cikin Zariya Zuwa Garin Dandume Jihar Katsina, bisani Aka iya ganin Karamar Motar cike da dankali sai Kuma wurin mutum biyu

Majiyarmu ya Shaida Mana cewa; wannan mutumin na Daya daga cikin Fasinjar Motar bisani jami’ai masu Sintiri Suka cafkesa bayan Kaddamar da bincike acikin motar har dai Suka iya gano Sababbin harsasai da Suka Kai mudu biyu a cikin bakar leda

Shi dai Wanda ake zargi da ta’addancin, ya bayyana cewa! Shi masana’ancine na wurin Shigo da motoci daga kwatono Zuwa Nijeriya, Amma tunda Gwamnatin Buhari ta kulle Hanyar Shigowa da Motoci Sai ya fada wannan Harkan

Acigaba da Zantawarsa da manema Labarai, ya Shaida masu cewa; wata matace take aikensa da ire-iren wadannan abubwan dako shi kansa Bai San ko meye acikiba Shi dai kawai umartansa akeyi ya Kai
Bayan Haka kuma Jami’an Sun binciki wayar hannunsa, nanma Suka ga Sakonnine manyan Kudi masu yawa

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button