Latest Hausa Novels

An Dakatar Da Babban Limamin Masallacin Rukunin Gidajen Ƴan Majalisu Dake Unguwar APO Abuja

An Dakatar Da Babban Limamin Masallacin Rukunin Gidajen Ƴan Majalisu Dake Unguwar APO Abuja….

An dakatar da Sheikh Muhammad Nuru Khalid daga limanci Saboda yin huɗuba Akan Rashin Tsaro da ya gabatar a jiya Juma’a Ɗaya ga watan Afrilu 2022.

Kwamitin kula da masallacin rukunin gidajen ƴan majalisu da ke unguwar Apo a Abuja, ya dakatar da babban limamin Masallacin Shiekh Nuru Khalid kan hudubarsa ta ranar Juma’a.

Sheikh Nuru Khalid a cikin hudubarsa ta ranar Juma’a 1 ga watan Afrilu, ya caccaki gwamnati kan kasa magance matsalar tsaro da kuma yawaitar kashe-kashe a Najeriya.

A cikin hudubar, malamin ya faɗi matakin da ya kamata talakawa su ɗauka idan har gwamnati ta bari aka ci gaba da kashe su, na kin fitowa zaɓe.

“Sharadin talakan Najeriya ya zama guda ɗaya kawai, ku hana kashe mu, mu fito zabe, ku bari a kashe mu, ba za mu fito zaɓe ba, tun da ku ba abin da kuka sani sai zabe,” in ji Sheikh Nuru Khalid a huɗubarsa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button