ylliX - Online Advertising Network An gano Ƙwan kunkuru wanda ya kai shekaru miliyan 90 a duniya. - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

An gano Ƙwan kunkuru wanda ya kai shekaru miliyan 90 a duniya.

An gano Ƙwan kunkuru wanda ya kai shekaru miliyan 90 a duniya.

An gano wani ƙaton ƙwan kunkuru mai ɓurɓushin halittu wanda aka yi imanin cewa kunkuru ne ya yi shi wanda yakai shekaru miliyan 90 da suka gabata.

Ƙwai mai girman ball na wasan tennis, wanda wani harsashi mai kauri ya ke karewa, a shekarar 2018 ne wani manomi a lardin Henan na ƙasar Sin ya gano shi, wanda ya aika zuwa wata jami’a domin gudanar da bincike.

An gano ƙwan kunkuru wanda ya kai girman ƙwallon tennis, wanda ke ɗauke da tayin da ya kusa ci gaba, a gabashin tsakiyar ƙasar Sin. Nanhsiungchelyids dangin kunkuru ne da aka samu a cikin ma’ajiyar Cretaceous a Asiya da kuma Arewacin Amurka.

Tawagar binciken, wacce ta haɗa da masana kimiyya daga Jami’ar Kimiyyar Geoscience ta ƙasar Sin da ke Wuhan, da gidan adana kayan tarihi na Henan da gidan tarihi na Royal Ontario na Canada, sun gudanar da gwajin CT-scan kan ƙwan.

Wannan ƙwan ɓurɓushin kunkuru wanda ya kai girman ƙwallon tennis, wanda ke ɗauke da tayin da ya kusa ci gaba, an gano shi ne a gabashin tsakiyar ƙasar Sin.

Yayin da aka samu ɗubban ƙwayaye na dinosaur a lardin Henan cikin shekaru 30 da suka gabata, Zelenitsky ya ce ba kasafai ake samun su cikin yanayi mai kyau ba.

Zelenitskythey ya ce mai yiyuwa ne wannan ƙwai ya tsira saboda kaurinsa da ba a saba gani ba, wanda ƙungiyar masu binciken ta auna girman inci 0.07, sau da yawa fiye da ƙwai na kunkuru Galapagos mai girman inci 0.01.

Idan aka yi la’akari da girman harsashin, tawagar ta yi ƙiyasin cewa wani kunkuru ne ya ajiye shi mai tsawon ƙafa 5.3, ma’ana daga wuyansa zuwa jelarsa, da ya fi tsayi fiye da tsayin wasu mutane.

Zelenitsky ya ce wani ɓangare na harsashi ya karye ne daga ciki, don haka yana yiwuwa ɗan tayin ya yi ƙoƙarin kyankyashe amma ya kasance a cikin harsashinsa tsawon shekaru miliyan 90.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button