LABARAI/NEWS

An kaddamar da shirin horar jami’an bijilantai 600 dabarun tunkarar yan bindiga gaba da gaba a Katsina

An kaddamar da shirin horar jami’an bijilantai 600 dabarun tunkarar yan bindiga gaba da gaba a Katsina wanda ya haɗa maza da mata a cikin wanna kwamitin

An kaddamar da fara shirin bayar da horo ga jami’an sintiri har su dari shida da suka fito daga ƙananan hukumomi 34 dake fadin jihar Katsina domin kawo karshen rikicin yan bindiga da kuma mazauna yan kin

An kaddamar da fara basu horon ne a sansanin horar da jami’an Sibil difense dake nan cikin birnin Katsina a wanna karon shine na farko domin samun sassauci matsin lamba da yan ta’addan daji ke wa mazauna ƙauyukan

Mai taimaka wa Gwamnan jihar Katsina a kan sha’anin tsaron Katsina ya ce an dakko mutum dari shidan ne a duk fadin jihar Katsina kuma maza da mata da suka aminta da samun horon da kashin kansu domin su fara aikin su

Ya ce tun da farko an fara ba yan bijilantai 500 irin wannan horon yanzun kuma 600 sun shiga nan gaba kuma za a kara jami’ai 1900 da za su sami irin wannan horon ya ce za a basu horon tunkarar yan bindiga ba sai sun shigo cikin garuruwa ba kuma za a basu horon koyon sarrafa makaman zamani

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button