ylliX - Online Advertising Network An Kama Ɗaya Daga Cikin Fursunonin Kurkukun Kuje A Katsina - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

An Kama Ɗaya Daga Cikin Fursunonin Kurkukun Kuje A Katsina

An Kama Ɗaya Daga Cikin Fursunonin Kurkukun Kuje A Katsina

Daya daga cikin fursunonin da suka tsere daga gidan gyaran hali na Kuje ya shiga a hannu a Karamar Hukumar Danmusa ta Jihar Katsina

Tserarren fursunan Kamala Lawal mai shekaru 33, ya shiga hannun jami’an ’yan sanda a garin Dan Musa a ranar Juma’ar nan Tawagar jami’an karkashin jagorancin DPO na Danmusa ce ta cafke Kamala bayan samun bayanan sirri

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isa ya shaida wa manema labarai hakan, yana mai cewa tserarren fursunan ya shiga hannu yana tsaka ta sayar tabar wiwi

SP Gambo ya ce da zarrar an kammala bincike a kan Kamala, rundunar za ta mayar da shi hannu Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta kasa

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button