ylliX - Online Advertising Network An kama dubban mutane bayan gano wagegen rami dauke da gawarwaki a Mali - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

An kama dubban mutane bayan gano wagegen rami dauke da gawarwaki a Mali

An kama dubban mutane bayan gano wagegen rami dauke da gawarwaki a Mali

Yan sandan Malawi sun kama ‘yan Habasha 72 da aka samu suna ɓoye a wani gandun daji a garin Karonga da ke arewacin ƙasar bayan gano wani wagegen rami cike dauke da gawarwaki 25.

An kuma kama ‘yan Malawi 10 wadanda ake zargi da hannu a safarar ‘yan Habashar zuwa cikin ƙasar.

A ranar Laraba ne gwamnati ta gano wani wagegen rami a wani gandun daji da ke lardin Mzimba cike da gawarwaki, inda kuma a kusa da wurin ne aka kama ‘yan Habashar.

An ruwaito cewa wasu matasa a yankin ne da suka je cikin gandun daji domin ɗiban zuma suka fara ganin gawarwakin mutanen a inda har wasu sun fara ruɓa, inda aka iya gano kawunansu da kuma ƴatsu bayan da matasan suka koma suka sanar da ‘yan sanda.

A safiyar ranar Alhamis ne aka kuma sake gano wani rami dauke da gawarwaki hudu kusa da wagegen rami da aka gano a ranar Laraba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button