ylliX - Online Advertising Network An Kama wani Mai Sayar da ruwa da laifin yin Jima'i da Matar Babban Ɗan Kasuwa a Legas. - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

An Kama wani Mai Sayar da ruwa da laifin yin Jima’i da Matar Babban Ɗan Kasuwa a Legas.

An Kama wani Mai Sayar da ruwa da laifin yin Jima’i da Matar Babban Ɗan Kasuwa a Legas.

Wani matashi mai shekaru 45 mai suna Chidi John mai siyar da ruwan Pure Water ya faɗa cikin matsala a jihar Legas bayan da ya je kai wa matar wani hamshaƙin ɗan kasuwa ruwan pure water sai matar ta ruɗe shi da yin lalata da ita

lamarin ya faru ne a titin Rasheed Balogun unguwar Isheri Olofin a Idimu Bayan maigidanta Mista Udeh ya samu labarin wannan mugun aiki uwargidan Misis Chika ta kuma bayyana cewa mai sayar da pure water Mista John yana lalata da ita ba tare da izininta ba daga watan Agusta 2022 har zuwa Oktoba 2022.

Mijin ya fusata ya je wurin yan sanda da ke Idimu inda ya kai rahoton cewa John ya yi wa matarsa ​​fyaɗe a gidan aurenta sannan ya buƙaci John ya biya shi miliyan 5.

A cewar makwabtan nasu rikicin ya fara ne bayan sun sanar da mijin cewa duk lokacin da zai tafi aiki matarsa ​​takan kawo John gidansa da karyar cewa tana ba da pure water sai su kulle kofa su zauna na tsawon sa’o’i kafin ya tafi

An ce mutumin Mista Udeh ya tambayi matarsa ​​game da lamarin amma ta musanta tun da farko kafin mijin ya tuntuɓi wani Fasto kuma ta amsa Ta bayyana cewa ta sha yin hakan ne da John wanda ake zargin ya yaudare ta da aikata hakan ba tare da amincewarta ba

A ƙarshe An bukaci John da Misis Chika su rubuta bayanai kan abin da ya faru a gaban yan sanda

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button