LABARAI/NEWS

An Kwantar Dashi a Asibiti Bayan Yayi Faɗa da Damisa

An Kwantar Dashi a Asibiti Bayan Yayi Faɗa da Damisa

 

Wani dan kasar Zimbabwe ya kwanta a asibiti bayan ya yi fada da wata damisa wadda ta kai masa hari a lokacin da yake gudanar da aiki a cikin daji

 

Da yake magana da kafafen yada labarai na cikin gida wanda abun ya shafa ya ce Yace abun ya faru ne a lokacin da nake aiki a wani fili da ke kusa da wani daji mai girman gaske

 

Na je ne don inbiya bukata na hango wasu gungun dabbobi kuma ban gane cewa damisa ne ke farautar su ba Ina cikin dabbobi amma ban taba tunanin akwai dabba mai hatsari a kusa ba

Na ji ana kara amma sai kawai na dauka babo ne suna cin wani abu da na juya sai na ga damisa ce

Ban ankara ba yayi tsalle ya kawomini hari sai na kamo kafarsa na gaba Na yi nasarar dauko dutse na buga a bakinsa

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button