ylliX - Online Advertising Network An Sanya Ranar Bikin Naɗin Sarautar Sarki Charles lll - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

An Sanya Ranar Bikin Naɗin Sarautar Sarki Charles lll

An Sanya Ranar Bikin Naɗin Sarautar Sarki Charles lll

Fadar Buckingham da ke Birtaniya ta ce za a yi bikin nadin sarautar sarki Charles lll ranar Asabar 6 ga watan Mayun shekara mai zuwa a majami’ar Westminster.

Sarkin zai kasance a majami’ar tare da matarsa Camilla, wacce ita ma za a nada ta a matsayin matar sarki wato ‘sarauniya Consort’ a bikin mai dimbin tarihi da za a gudanar.

An dai nada Sarki Charles lll a matsayin sarki Birtaniya bayan rasuwar mahaifiyarsa Sarauniya Elizabeth ll, to amma bikin nadin shi ne alamar murna ta farko a matsayinsa na sabon sarki.

A yayin taron za a dora wa sarkin kambin sarauta a kansa, a matsayin mutum mafi karfin iko da matsayi a Birtaniya.

Bikin nadin da za yi a shekara mai zuwa, shi ne irinsa na farko cikin shekarar 70, kuma na farko da za a yi ranar a Asabar tun bayan na sarki Edward VII da aka yi a shekarar 1902.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button