LABARAI/NEWS

An Tabbatar Mutuwar Mutum Hudu Da Ruftawar Gini a Fashewar Silindar Gas a Unguwar Sabon Gari Dake Jihar Kano

An Tabbatar Mutuwar Mutum Hudu Da Ruftawar Gini a Fashewar Silindar Gas a Unguwar Sabon Gari Dake Jihar Kano

A yau 17/05/2022 da karfe 10 na safe an ji karar fashewar wasu abubuwa da ake kyautata zaton bam ne kusa da Kotu road a unguwar Sabon Gari dake Kano.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko, fsi, yace bayan samun rahoton ya jagoranci tawagar rundunar ta hadin gwiwar zuwa wurin da lamarin ya faru a wani gini da ke lamba 01, Aba/Court Road, Sabongari Quarters Kano daura da Winners Kids Academy.

Ya kuma kara da cewa ‘An killace wurin da ake zargin fashewar wani abu ne da ya kai ga rugujewar gini, sannan kuma wasu hudu da suka mutu (Maza 3 da Mace 1) an cire su aka garzaya da su asibitin kwararru na Murtala Mohammed Kano, inda likitan ya tabbatar da sun mutu.

A binciken farko da rundunar yan sanda ta gudanar ya bayyana fashewar silindar gas ce ta fashe. Sai dai kafofin yada labarai da dama da ma sauran al’umma na ganin kamar bam ne ya fashe amma ba a son fadan hakan saboda gudun tashin hankali.

Wasu na ganin kamar rundunar yan sandan ta jihar Kano ta yi saurin fitar da sakamakon binciken ta na farko, saboda dalilai kamar haka:

  1. Gas na fashewa ba tare da wuta ba?
  2. Silindar iskar gas na da karfin rusa gini?

Amsa wadannan tambayoyi sune zasu tabbatar da sahihancin wannan binciken.

Mene ne ra’ayin ku?

Jaridaradio 17/5/2022

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button