LABARAI/NEWSLatest Hausa Novels

An Tsinci Gawar Matashi A Cikin Kwata A Kano

An Tsinci Gawar Matashi A Cikin Kwata A Kano

Kwatar da aka tsinci gawar matashin a Kano

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

An tsinci gawar wani matashi mai kimanin shekaru 25 mai suna Ghaddafi Saleh a cikin wata kwata da safiyar Laraba a Jihar Kano. Lamarin ne a unguwar Kundila kan titin Zariya daura da asibitin dabbobi.Yadda Hana Tukin Adaidata Sahu Da Daddare Zai Shafi Rayuwarmu — KanawaA zantawar manema labarai da wani matashi kuma mazaunin yankin, Sultan Bello, ya ce ruwa ne ya koro gawar mutumin ya kawo ta wannan waje. Ya kuma ce, “Wannan ba shi ne karo na farko ba da ake tsintar irin wannan gawar, na uku ke nan cikin kwanaki hudu da suka wuce.” A nasa bangaren, mai magana da yawun Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Yusuf Abdullahi, ya tabbatar da rasuwar matashin, inda ya ce tuni suka mika gawar ga ofishin ’yan sanda da ke Titin na Zariya Road a Kano. Ya kara da cewar mamakon ruwan da aka yi ranar lahadi shi ne musabbabin faruwar hakan.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button