LABARAI/NEWS

Ana Zargin Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Kontagora da yin Awon gaba da Akwatin Zabe

Ana Zargin Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Kontagora da yin Awon gaba da Akwatin Zabe

Wasu al’umma ne suka koka akan yadda aka samu matsaloli Yayin Gudanar da Zaben Kananar Hukumomin Kontagora, inda suke zargin mataimakin shugaban ƙaramar Hukumar Kontagora, Aliyu Makiga da yin awon gaba da akwatin zaɓe, a wani rumfar zaɓe dake rafin Karma Gundumar Nagwamatse.

 

 

Ɗaya daga cikin wakilan jam’iyyar NNPP a mazaɓar Rafin Karma Yayi zargin cewa bayan an dauke akwatin zaɓen a motar mataimakin shugaban ƙaramar Hukumar aka sanya akwatin daga bisani kuma suka cikawa motar iska.

Wakilin mu da ya tuntuɓi Aliyu Makiga akan zargin da akeyi masa yace shi ba zai ce uffan ba akan wannan al’amari.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button