ylliX - Online Advertising Network Anbiyashi 5000 da kwanon Shinkafa ya aikata kisan kai a Jihar Adamawa - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Anbiyashi 5000 da kwanon Shinkafa ya aikata kisan kai a Jihar Adamawa

Anbiyashi 5000 da kwanon Shinkafa ya aikata kisan kai a Jihar Adamawa

Wani mutum a adamawa ya bankawa ango da amarya wuta saboda amaryan ta yaudareshi bayan sunyi alkawarin aure Wanda aka baiwa aikin kisan ya aikata hakan bayan biyanshi nera dubu biyar da kwanon shinkafa 4

An tattaro cewa Ibrahim wani magidanci ne mai yara hudu amma yafada rudin soyayya da amaryan harya kashe mata kudi naira 150, 000 bayan sunyi alkawarin aure Ibrahim ya baiwa savanna aikin banka wuta cikin daren ranan 6 ga watan satumba 2022

Wannan abu ya farune makonni biyu kacal bayan auren amarya da ango Wata jarida ta rawaito cewa amaryan ta mutu a asibiti sakamakon raunuka data samu a gobaran yayin da shikuma angon yana asibiti rai hannun ubangiji

Kakakin hukuman ‘yan sandan jahan SP Suleman Ngoruje, ya tabbatar da afkuwan lamarin inda yace an kaddamar da bincike kuma za’a gurfanar dasu a kotu Ya bada labarin cewa lallai za’a hukunta mutumin kuma kada mutane su dauki doka a hannun su.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button