Videos

Anya kuwa murja ba maula takeyi a wajen Kwankwaso ba kuwa ?

Anya kuwa murja ba maula takeyi a wajen Kwankwaso ba kuwa ?

Jarumar kammywood kuma fitacciyar yar tiktok wato murja Ibrahim kunya ta fito ta fadi matsayar ta akan zabe me zuwa wanda ga dukkan wasu alamu suka nuna jarumar tana bayan jagoran siyasar kwankwasiyya wato Senater rabi’u Musa Kwankwaso

Sai dai wasu na kallon bawai ta fadane har cikin rantaba kawai ta fadane a iya baki domin mutane dayawa suna ganin kamar kwankwason ba Lallai yakai labari ba a zabe me zuwa domin jam’iyar tasa har yanzu bata shiga zuciyoyin al’umma ba saboda sabuwa ce bata dadeba

Tace a nata tunanin babu wani mutum dayafi chanchanta a zabe kamar sa domin ayyukan da yayi a garin Kano lokacin yana gwamna kuma da yadda yake da yawon masoya da magoya baya

Murja tace ita har cikin ranta kwankwaso ne wanda ya dace da jama’a su zabe domin babu wani wanda yake da nagarta da kuma halin kirki kamar sa idan aka duni yadda yake taimakon yayan talakawa

Sai dai kuma mutane suna ganin kamar wannan jarumar maula ce kawai tasa ta fadi wa’yannan maganganun saboda da bata taba fadar haka ba sai yanzu

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button