LABARAI/NEWS

Anyi Garkuwa Da ‘Yan Gusau 50 Da Sukaje Daurin Aure Sokoto A Ranar Asabar

Anyi Garkuwa Da ‘Yan Gusau 50 Da Sukaje Daurin Aure Sokoto A Ranar Asabar

Yan bindiga dake kauyan sokoto sun yi garkuwa da mutane 50 da suka halarci bikin Aure a Sokoto lokacin da suke komawa Gusau ta Jihar Zamfara a ranar Asabar

Shaidun gani da ido sun ce da yammacin jiya Asabar Yan bindigar suka tare hanyar lokacin da masu bikin ke komawa garin Gusau inda suka bude wuta akan daya daga cikin motocin dake cikin tawagar su abinda ya tilasta musu tsayawa

Rahotanni sun ce tawagar masu bikin ta fito ne daga Tambuwal lokacin da take komawa birnin Gusau kuma nan take Yan bindigar sukayi garkuwa da matafiyan suka gudu da su cikin daji

Yankin Arewa maso yammacin Najeriya Musamman Jihar Zamfara da Sokoto na ci gaba da fuskantar hare haren ‘Yan bindiga wadanda ke kashe matafiya da mazauna karkara tare da garkuwa da wasu domin karbar diyya

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button