ylliX - Online Advertising Network Anyi kira Ga Hukumomin tsaro da na addinin musulunci da su ɗauki matakin da yakamata ga jarumar Hausa mai Suna Rahama sadau. - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Anyi kira Ga Hukumomin tsaro da na addinin musulunci da su ɗauki matakin da yakamata ga jarumar Hausa mai Suna Rahama sadau.

Anyi kira Ga Hukumomin tsaro da na addinin musulunci da su ɗauki matakin da yakamata ga jarumar Hausa mai Suna Rahama sadau.

Kiran ya fito ne Daga Kungiyoyin kare mutuncin addinin musulunci da Kuma Yan Gwagwarmaya Daga Cikin Masu korafi Game da Rahama sadau akwai Malam muhammad Lawal Gusau Wanda shugaban wata makarantar islamiyya Ce Dake Gusau a Jihar zamfara.

Rahama sadau dai ta karbi wata Girma mawa Daga kasar India Wanda Kuma ke ɗauki da Gunki Wanda Hakan ya Saba da koyarwa ta addinin musulunci.

Muhammad Lawal Gusau ya nuna takaicinsa tare da yin kira ga Musulumi suyi Allah wadai da wannan karramawa da akayiwa Rahama sadau Karbar kyautar Gunki ya Saba da addinin musulunci Wanda a tarihi anga yadda annabi Muhammad saw ya yaki Masu bautawa gunkin.

Haka Kuma tarihi ya Bayyana cewa wasu jaruman kasar India sunki karbar irin wanann kyautar sakamakon tana dauke da Gunki

Daga Cikin wadanda suka ki Karbar kyuatar akwai Akwai marigayiya Lata Mangeshkar, da Aamir Khan, Kangana Ranaut da Imran Khan da Kasar Pakistan kuma shahararren dan wasan kwallon Gora (hockey) saboda irin akidar su da kuma son addinin su.

To Amma abin takaici shine yadda Rahama sadau ta karbi Wannan kyauta duk da cewa ita musulma Ce.

a shekara ta 2020 dai sai da muhammad Lawal Gusau ya taba shigar da korafi ga Babban sifetan yan sanda na Kasa a wancan lokaci Kuma aka cimma matsaya sakamakon Wani Rubutu da akayi a shafinta na Twitter Wanda ya zama batanci ga addinin musulunci.

Muhammad Lawal Gusau yace zasu Kara Mika kokensu ga Hukumomin kasar nan akan irin wadannan dabi’u, da Akeyi Wanda yake cin fuskane ga musulunci.

Yayi Allah wadai da karbar Wannan kyauta Kuma ya nuna cewa musulamai su kyamaci kyautar.

Muhammad Lawal Gusau yayi fatan samun cigaba da zaman lafiya tare da kira ga Hukumomi suyi abunda ya dace Dan gudun abunda kaje yazo.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button