Nishadi

Aure zan Kara : Adam A zango ya firgita matar sa da maganar aure

Adam A zango ya firgita matar sa ta hanyar bayyana ma ta cewa zai Kara aure lamarin da ya haifar da rudani a tsakanin su

Fitaccen jarumin masana’antar kannywood Adam A zango a wani fefan bidiyo da ya wallafa a shafin sa na sada zuminta ya nuna yadda ya firgita matar sa

Jarumin a wani salo na mamaki ya bayyana wa matar sa cewa yana daf da Kara aure lamarin da ya matukar girgiza ta Hadi da firgita ta

Wannan magana da jarumin kannywood din yayi was matar tasa yasa ta shiga wani mahuyacin Hali Inda ta Daina har cin abinci sakamakon wannan magana ta Karin aure

Bayan duba da halin da yaga matar tasa ta shiga da Kuma Wanda take son dorawa kan yasa jarumin fayyace ma ta komai inda yace mata da wasa yake

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button