Latest Hausa Novels

Azumi me Dadi (Ramadan 2022)

Azumi Azumi me Dadi

Barka da shan ruwa ga ɗaukacin zaɓaɓɓun bayin da Allah yaiwa arzikin azumtar wannan rana ta alhamis 14/8/1443AH

Ina roƙon Allah (SWT) ya karɓi ibadun mu, ya albarkaci rayuwarmu, yasa mun amfana da ibadun da mukai, Allah kasa addu’oin da muke su amfane mu.

┈┉┅━━┅┉┈┈┉┅━━┅┉┈

Cikin ikon Allah Sha’aban zai raba a gobe Jumma’a WANDA hakan ke kawo ƙarshen azumin Nafilar wasu cikin mu na wannan shekarar😢, domin azumin Nafila irin wannan shi kusan a iya cewa shekarar sa na cika ne idan Ramadan ya iso, domin ba’a Nafila a Ramadan, bayan Ramadan kuma shirine sabo na dora Azumin Nafilar zuwa wani Ramadan ɗin ga me nisan kwana😢
┈┉┅━━┅┉┈┈┉┅━━┅┉┈

Masu azumtar ranakun 13,14 da 15 na kowanne wata, da kuma wanda basu saba da azumin Litinin da alhamis ba kurum de suna yinsa ne jefi jefi randa suka sami iko wataran Alhamis wataran su azimci Litinin! Babu consistency…. Toh duk wannan ina me tunasar daku cewa daga gobe azumin Nafila ya sauka daga kanku sai bayan Ramadan.

┈┉┅━━┅┉┈┈┉┅━━┅┉┈

Domin kwai hadisi ingantacce cikin Abu Dawud me lamba ta (3237), al-Tirmidhi (738) da hadisin Ibn Najah (1651) Wanda Abu Hurayrah ya ruwaito daga annabi (SAW) cewa ya haramta ga mutum ya azimci sha’aban idan bayan watan ya raba. Ma’ana ya ketare 15, Sai in ahali guda biyu:

  1. Kode wanda ya saba halinsa ne azumtar Litinin da alhamis akai akai
  2. Ko me azumtar 13,14, da 15 na kowanne wata wanda suka auko aciki.

Duk wanda baya cikin kaso biyun can toh daga yau ya gama azumin Nafila.

┈┉┅━━┅┉┈┈┉┅━━┅┉┈

Wanda kuma ya saba azumtar litinin da alhamis toh shima yana da inda aka dakatar dashi: Ba’a azumin Nafila kasa da kwana biyu kafin Ramadan. Kamar yadda hadisin abu Huraira cikin Al-Bukhari (1914) da Muslim (1082) ya ruwaito

Hakama hadisin Nana Aisha
cikin Al-Bukhari me lambata (1970) da Muslim me lamba ta (1156)
Yazo cewa annabi (SAW) na rage kididdigaggun kwanaki kafin RAMADAN batare da azumi ba, duk da bata kididdige yawan kwanakin ba amma de anan ne MALAMAI suka tafi akan cewa baki ɗaya bai halasta ai azumin Nafila ƙasa da sati 1 kafin Ramadan ba.

Saboda anaso ai amfani da ragowar kwanakin aima imani da jiki caji, ai shiri, asami karfin jikin da za’a tunkari ramadan.

┈┉┅━━┅┉┈┈┉┅━━┅┉┈

Don haka da wannan nake tunasar damu masu azumtar Alhamis da Litinin ko yaushe cewa muma rana ita yau (Alhamis) insha Allahu in muna da rai zamu kawo karshen namu azumin nafilar.

Don haka saura 2 ya rage muna.

Allah SWT kasa mun amfana, kasa muna da rabon kaiwa bayan Ramadan, idan kuma wannan shine azumin Nafilar mu na karshe ya Allah duk abinda muka roka ka bamu.

Rayuwa kenan😢 sai kaga abu kamar da wahala, amma kana waigawa sai kaga komi lokaci ne. Allah ka qara muna fahimtar addini.

👂🏼
Wanda ake binsu bashin azumi kuji tsoron Allah kui maza ku biya, kwai sakaci da raina addini ka shafe watanni 10 batare da ka biya azumi ba har sai Sha’aban ya shigo, gaskiya kuiwa kanku faɗa. Kofa kun Mutu ba’a yafe muku ba, sai ansaku a wuta.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button