Daga Malaman mu

HUKUNCIN RAMUKON AZUMIN MACE MAI SHAYARWA

HUKUNCIN RAMUKON AZUMIN MACE MAI SHAYARWA :

TAMBAYA TA 2951
*******************
Assalamu alaikum wa rahmatullah.

Malam barka da safia ya fama da jama’a? ya kuma iyali?.

Tambaya garemu
Mace ce cikinta ya tsufa bata iya yin azumin ramadana ba, Ta haihu afarkon watan shawwal.
Yanzu kuma tana shayarwa, kuma dalilin yawan tsotson da yaron keyi bata samu yin ramuwa ba.
Gashi wani Ramadhan din ya tunkaro in muna raye. Shin zata iya ciyarwa ne ko kuwa lallai azumin zata rama?.

Kuma in ramuwar yakai ramadhan din meye hukuncin? Allah ya saka da alkhyri amin.

AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Wannan mas’ala ce wacce Malamai sukayi sa’bani sosai akanta. Amma dai ga ka’dan daga cikin abinda na fahimta atakaice :

Idan mai ciki ko mace mai shayarwa tasha azumi, saboda tsoron lafiyarta ko lafiyar jaririnta, Imamu Malik yace ita mai ciki zatayi ramuko ne kawai. Amma mai shayarwa zata ha’da ciyarwa da ramuko. Awata riwayar kuma yace ramukon ka’dai zatayi.

Imamush Shafi’iy da Imamu Ahmad bn Hanbal sunce: Zasu ciyar da Mudun Nabiy ﷺ guda bisa kowanne wuni, sannan kuma zasuyi ramuko. Shi kuwa Imam Abu Hanifa yace ramuko kawai zasuyi.

Amma akwai wata fatawar daga Abdullahi bn Umar da Abdullahi bn Abbas (Allah ya yarda dasu) sun ce a irin wannan ranayin, da mai cikin da mai shayarwar, ciyarwa ka’dai zasuyi ba tare da ramuko ba. (mudun Nabiy ﷺ biyu bisa kowanne wuni guda).4

Don Qarin bayani aduba : Al Mugniy na Hafiz Ibnu Qudaamah Almaqdisiy, da kuma Rahmatul Ummah Fikhtilafil Ayimmah (shafi na 113).

DAGA ZAUREN FIQHU 07064212990 (08/06/1443 11/01/2022)

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button