LABARAI/NEWS

Ba fa zan wofantar da alkawuran da nayi maku ba ‘Yan Najeriya: BUHARI

Shugaba Muhammad Buhari ya bayyana cewa fa shi sam ba zai yiwu ya wofantar da alkawuran da yayi ma ‘yan Najeriya ba lokacin neman zabensa, kuma sai ya cika su duka kafin ya sauka daga kan mulki.

 

Sugaban ya bayyana hakan ne a sakonsa na bukin Kirsimeti da ya zayyana ma ‘yan Najeriyan, sannan ya kara da cewar yana taya kafatanin Kiristocin Najeriya murnan shagulgulan bukin kirsimetin kamar sauran mabiya na duniya.

 

A cikin sakon, Shugaba Buhari ya roki ‘yan Najeriya da su daure su yi allurar Annobar Korona, domin kaucewa yada cutar a cikin al’umma.

 

Game da tsaro kuma, shugaban ya bayyana cewar har yanzu dai akwai kalubale, duk da cewar jami’an tsaro na samun nasarori.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button