LABARAI/NEWS

BA MA FATAN YAKIN DUNIYA

BA MA FATAN YAKI A DUNIYA

Bayan da Amerika ta ingiza Kasar Ukraine suka fara yaki da Kasar Russia watanni 6 da suka gabata kusan kowace Kasa a duniya sai da illar yakin Russia da Ukraine ya shafeta

Wasu zasu ce har nan Nigeria eh tabbas har nan Nigeria sai da yakin Russia da Ukraine ya shafemu sosai ya cutar da mu A duniya ba Kasar da ta kai Ukraine noman alkama, ba kuyi mamakin abinda yasa fulawa yayi tsadan da bamu taba ganin irinsa ba a tarihin Nigeria

idan an shiga yanayin damina irin wannan a Arewa da komai ya koma gona, abinci yayi tsada, talaka fulawa yake iya saya da araha yaci, to yanzu fulawan ya ma fi sauran kayan abinci tsada, yakin Ukraine ya haddasa, saboda Ukraine bata samun damar fitar da alkama da sauran kayan amfanin gona saboda yaki

Kasar Russia ta dena fitar da gas wanda yankin turai gaba daya suka dogara da shi, hakan ya sa Kasashe irin namu farashin kudi mu ya karye, Dala tayi tsada, farashin kayan masarufi yayi tsada, wannan tsadar rayuwar ya shafi kusan kashi 90 cikin 100 na Kasashen duniya

Ana cikin wannan halin kuma, sai ga Amurka tana kokarin kunna wutar yaki tsakanin Kasar Taiwan da Kasar China, Kasar China na ikrarin Taiwan mallakinta ne, mahukuntan Taiwan kuma sun hade kai da Amerika, har ma sai gashi Kakakin Majalisar dokoki na Kasar Amurka Nancy Pelosi ta ziyarci Taiwan a jiya duk da gargadin da Kasar China ta yi

China tana ganin alakar Amerika da Taiwan barazana ne gareta, kamar yadda Russia ta dauki alakar Ukrain da Amerika a matsayin barazana da kuma mamaya ta karkashin kasa

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button