LABARAI/NEWS

Baban Hafsan Sojojin Ƙasa Ya Ƙaddamar Da Tallafin Gidaje Sittin Ga Sojoji

Baban Hafsan Sojojin Ƙasa Ya Ƙaddamar Da Tallafin Gidaje Sittin Ga Sojoji

Babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya Laftanar Janar Faruk Yahaya ya ƙaddamar da rukunin gidaje 5 guda 60 na gidaje domin sauƙaƙa wa sojoji masu muƙamin Kofur da ƙasa ƙarancin masauki a garin Fatakwal na jihar Ribas.

Janar Yahaya ya ƙaddamar da rukunin gidajen kwana a jiya Litinin 17 ga Oktoba, 2022, yayin da ya kai ziyarar aiki a yankin na 6 Division of Responsibility.

Da yake jawabi a lokacin ƙaddamar da sabbin tubalan ginin, COAS ya lura cewa sabon aikin da aka kammala zai kawo tallafi ga ma’aikata, domin yana basu wurin zama da sauran ababen more rayuwa. Ya kuma yi kira ga sojojin da su kara himma da kwazo domin samun nasarar tabbatar da ayyukansu yadda ya kamata.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button