LABARAI/NEWS

BABBAR MAGANA Jarumin Kannywood Baba Ari Ya Lakaɗawa Malamar Islamiyya Duka Saboda Ta Hukunta Ƴarsa

BABBAR MAGANA Jarumin Kannywood Baba Ari Ya Lakaɗawa Malamar Islamiyya Duka Saboda Ta Hukunta Ƴarsa Na rantse da Allah gefen ɗankwalinta kawai na doka, inji shi

Ana zargin shahararren ɗan wasan barkwancin nan na masana’antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood, Aminu Ali wanda aka fi sani da Baba Ari da lakaɗawa wata malamar Islamiyya dake yankin Ƙofar Nasarawa a jihar Kano duka, bisa hukunta ‘yarsa mai suna Hafsa da malamar ta yi a makaranta, sakamakon laifi da suka aikata

Malama Safiya Nasir, wacce ake zargin Baba Ari ya jibga, ta bayyana cewar ina zaune a cikin Aji na biya musu karatu sai yarinyar ta ke cin cingam tare da wata ɗalibar a kusa da ita bayan kuma dama wani malami mai suna Malam Sulaiman yayi musu magana, saboda haka na ɗauki bulala na daki ta kusa da ita, amma ita Hafsa sai ta ce ba za’a dake ta ba

har mukayi sa’insa ina fara yi mata bulala sai ta zube a ƙasa wanwar da nufin ta tayar da Aljanu
Daga nan ina cikin tafiya sai ga mahaifinta ya zo ya na cewa, ke Hafsa waye ya doke ki, wacce malamar ce ta doke ki? Ana faɗa masa kawai sai ya janyo ni ya kifa min mari, ya fara taka bayana da takalminsa inji ta

Sai dai a nasa ɓangaren, Baba Ari yace ya yarda ya yi kuskure, kuma ya amsa laifin sa, amma yayi rantsuwa da mahalicci akan cewa, gefen ɗankalinta kawai ya doka

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button