Latest Hausa NovelsFadakarwaLABARAI/NEWS

BABI CIKIN BAYANIN RAFKANNUWA

BABI CIKIN BAYANIN RAFKANNUWA
:::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::

Rafkannuwa acikin sallah nada hukunce-hukunce, wanda gaskiya komi iya karatun sallar mutum inbai sansu ba bai kamata yai limanci ba. Da yawa kan ɗauka koya akai sallah tayi amma fa ba haka bane.

Sujudi sahwi sune sujjadu iri biyu da ake yayin da aka sami rafkannuwa. Wato:

  1. Sujjada Ba’adi
  2. Sujjada Qabli

┈┉┅━━┅┉┈┈┉┅━━┅┉┈

SUJJADA QABLI:

Ana yinta ne idan Mutum yayi ragi acikin sallah. Wato misali ace sallah me raka’a 4′ mutum I ya Mance yai sallama a iya raka’a ta 3. Toh anan sai mutum ya maida goshi ƙasa yai sujjada guda biyu bayan yai sallama.

SUJJADA BA’ADI: Ana yinta ne idan mutum yai qari acikin sallah. Wato misali sallah me raka’a 2 mantuwa tasa mutum yai raka’a uku ‘3’.

Toh sai yai sujjada guda biyu ‘2’ bayan yai zaman tahiya amma kafin yai sallama zai yisu.

┈┉┅━━┅┉┈┈┉┅━━┅┉┈

MA’ANA DE

Kamar yadda Malam me ahalari yace; Kowacce sujjada bayan yinta sai kai karatun tahiya kafin kai sallama, saɓanin wasu mutanen da zarar sukai sujjadar kawai saide sui sallama, amma nassi ingantacce ana yi musu tahiya suma kafin sallah.

BA’ADI; ana yinta bayan anyi sallama daga sallar da akai, ita kuma
QABLI; ana yinta ne kafin sallame sallar da ake ciki.


◼️Wanda duk Qabli ta kamasa a sallah amma sai duk da haka ya manta bai tuna ba har sai bayan ya idar da sallar wato yai sallama… alhalin Qabli kafin ai sallama ake yinta,
Toh hukuncin sa ana shine: Sai yai sujjadar bayan sallama (ba’adi).

Idan kuma andaɗe ko har ya fita daga masallaci ko gurin da yai sallar sannan ya tuna… Toh sujjada ta ɓaci, sallar ma ta ɓaci matukar abinda ya tauye a sallar sunkai sunnoni uku zuwa sama. Amma idan sunnonin Basu kai uku ba toh shikenan sallarsa tayi babu komi kansa.

Don haka in mun mance mu daure mu koma musan sunnonin sallar, mustahabbai da farillai, banason kawo su tunda kun fiye korafin rubutu na tsayi, amma de kusani wannan shine ya kawo mu duniya in sallah bata cika anyi aikin banza.


◼️Wanda kuma ya Mance SUJJADA BA’ADI, Tohfa sai ya ramata koda anshekara sanda ya tuna.

◼️Wanda kuwa ya tauye farilla a cikin sallah toh sujjada Qabli ko ba’adi kadai basa wadatar wa dole zai canza sallah.

◼️Wanda ya Mance mustahabbi a sallah babu sujjada agareshi.

◼️Wanda yai zance ko magana cikin sallah bisa mantuwa ko rafkannuwa shima zai SUJJADA BA’ADI

◼️Wanda yai sallama daga raka’a ta biyu da rafkannuwa shima zai sujjada Ba’adi. Bayan ya ciko sauran.

◼️Wanda ya qara raka’a 1 ko 2 shima zai sujjada Ba’adi.

◼️Wanda ya qara kwatan-kwacin raka’oin sallar da yake MISALI; asuba me raka’a 2 sai ya manta yai raka’a 4 wannan sallar ta ɓaci. Sai ya canza wata.


◾Wanda ya maimaita Fatiha acikin sallah bisa rafkannuwa toh zai yi sujjada Ba’adi.

◾Wanda yai nuni da hannunsa ko da kansa acikin sallah babu komi agareshi sallarsa tayi.

◾Wanda yana sallah yaji an ambaci sunan annabi (AS) kuma yace amsa da fadin sallallahu alaihi wasallam, shima sallarsa tayi babu komi kansa koda yana sane ya amsa.

◾Wanda ya karanta surori 2 ko fiye da haka cikin raka’a ɗaya, ko ya fita daga wata surar zuwa wata surar, ko yai ruku’u kafin cikar surah, ko ya datsi ayoyin karshen surah kai tsaye duk babu komi kansa, sallah tayi

◾Wanda ya tuna bai karatun surah ba bayan ya sunkuya zuwa ga ruku’u toh bazai dawo gareta ba, sallarsa tayi kuma babu komi kansa.


🔳Wanda kuma ya tuna asirtawa ko bayyanawa kafin ya tafi ruku’u…
(misali yana shirin duqawa sai ya tuna kash ashe aboye nai karatun sura alhali magariba nake yi) toh kada ya duqa kurum ya sake karatun surar a bayyane. Kuma koda yai sallama babu sujjadar komi kansa.

🔳Idan kuwa kafin yai ruku’u tunawa yai kash ashe a bayyane nai karatun Fatiha alhalin azahar nake yi) toh tunda bai kai ga duqawa ba nan ma zai zubar da karatun baya, ya qara maimaita Fatiha a asirce… Idan ya idar yai sallama toh zayyi sujada Ba’adi, domin Fatiha farilla ce a sallah.

🔳Wanda yai dariya a sallah nan ma sallarsa ta ɓaci koda da rafkannuwa ne ballantana da gangan. Sai ya canzota gaba ɗaya.

🔳Wanda yai yunkurin mikewa tsaye daga sujjada alhalin raka’a ta biyu ce da ya dace ya zauna… Toh idan ya tuna tun kafin hannayensa da guiwoyinsa su rabu da ƙasa toh sai ya komo ya zauna, kuma babu sujjadar komi kansa

🔳Idan kuwa hannuwansa da guiwoyinsa sun rabu da ƙasa yakai ga mikewa sannan ya tuna toh anan bazai dawo ya zauna ba, zai zarce, amma kafin yai sallama zai yi sujjadar da ake kafin sallama wato SUJJADA QABLI

🔳Idan kuma bayan da ya miƙe ya daburce takai ga ya dawo ya kuma zaunawa kilama limanci yake saida ya mike yaji ana subahanallahi…. Domin nusar dashi, toh in bai dawo ba kuma mamu ku bishi ayi QABLI, amma idan rafkannuwa tasa ya dawo ya zauna toh nan ma bakomi saide bayan anyi sallama zakui Sujjada BA’ADI tare dashi, inma kai kadai ne de ka tuna kuma ka dawo ka zauna maimakon cigaba da tsayuwa toh Ba’adi zakai.


◼️ Wanda yai kokonton tsarki ko najasa har takai ga yayi tunani ɗan kaɗan acikin sallah kuma ya gano cewa eh yana da tsarki ko kuwa ba najasa tare dashi ko tufafinsa… Toh babu komi kansa.

◼️ Wanda yai waige cikin sallarsa da rafkannuwa babu komi kansa. Idan da gangan ne waigen toh makaruhi ne, amma idan ya zamto da gangan kuma waigen yakai ga har ya juyawa alkibla baya wato fuskarsa ta kallo yamma alhalin gabas ce alkiblarsa toh ya yanke sallah ya somo wata daban.

◼️ Wanda yai salla da alhariri ko zinare, ko yakai hannu yai sata acikin sallah ta hanyar dafe kayan wani ko takesu ya ɓoye ko ya kalli abinda yake haramun ne kallonsa… Toh shi mai saɓo ne, amma sallarsa tayi.

◼️ Wanda yai gyangyadi cikin sallah babu komi kansa, idan kuma bacci yai nauyi cikin sallah toh sai ya canza alwala.

◼️ Wanda yai gatsali cikin karatun sallah da wata kalma wacce bata Kur’ani ba toh zai yi sujjada BA’ADI wato bayan sallama.

Idan kalmar da yai gatsalin da ita ta Kur’ani ce babu sujjada kansa, saide in lafazin ya sauya ma’anar kalmar toh sallah ta ɓaci.


◾Idan mutum yabar aya ɗaya acikin Fatiha toh zai yi sujjada kafin sallama wato Qabli. idan kuwa yafi aya ɗaya to sallah ta ɓaci.

◾Nishin mara lafiya cikin sallah abin gafartawa ne, gyaran murya abin gafartawa ne, idan kuma gyaran muryar na nuni ne wannan makaruhi ne amma de sallah bata ɓaci ba.

Allah shine Masani.

Allah ka karɓi sallolin my ba don mun iya ba ya Allah, kurakuran mu ka yafe mana.

✍🏻
Ibrahim Y. Yusuf

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button