Daga Malaman mu

BABU KABILAN CI KO NUNA BANGARAN CI A RAYUWAR FULANI,

BABU KABILAN Ci KO NUNA BANGARAN CI A RAYUWAR FULANI,

 

Alummar Fulani itace Kabila daya tilo a Africa da bata da Dabi’ar kabilanci ko nuna bangaran ci ko wani Abu mai kama da haka,

 

Alummar Fulani kanyi rayuwa a duk inda suka tsinci Kansu kuma A cikin kowace Irin Alumma batare da Sun dauki Alummar da suka tsinci kan su a ciki a matsayin wasu daban ba,

 

Fulani basa taba nuna kyama ko kabilanci ga duk Wanda ya rabe su, ko daga wane addini yake kuma ko daga wace kabila yake,

Maimakon hakan Fulani kan Nuna so kauna da Girmamawa ga duk Wanda ya rabe su , Wanda har ta kai Fulani suna daukar ‘ya’yansu su Bawa duk Alummar Suka tsinci Kansu a cikin ta,

 

Hakan ba boyayyen Abu bane game da Fulani, Sam basu San wani Abu kabilanci ba, fulani kan dauki duk Dan Africa Dan uwa ne, muddin karabe su to za su Nuna ma so tare da daukar sunan su wato Iyayen Africa,

 

Azahiri yake FULANI su sukafi kowace kabila Auratayya tsakanin su da wasu kabilu a Africa, Fulani su sukafi Kowace kabila Yaduwa a Africa, Fulani su sukafi kowace kabila yarda cewa Kasa daya Alumma daya,

 

Duk da matsayin da Fulani ke da shi, Amma domin nesan ta Kansu da kabilanci sukan Aje Al adun su yaren su, Tarihin su su dau na Alummar da suke cikin ta. Wanda babu wata kabila a Africa da take hakan ,

 

Saboda haka Fulani babu Kabilanci a Tsarin rayuwar su, tuntuni Masana Suka yi batu akan hakan,

Domin Fulani sun yi karfi tare da kafa manyan dauloli a Africa batare Nuna wannan mummunar Dabi’ar ba,

 

Alhamdullah duniya tasan kyakyawan tushe da tarihin FULANI Kuma tarihi da hali ai zanen dutse ne ,

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button