LABARAI/NEWS

Babu Samun Nasara Babu albarka ga Gwamnatin Buhari, Ko Kun San dalili?

Ko kun gamsu da wannan bayanin?

Babu Samun Nasara Babu albarka ga Gwamnatin Buhari, Ko Kun San dalili?

Bisa tsarin ko wanne irin addini da al’ada tare da kowanne irin nau’in Bil’adama ya aminta da cewa cin amana na haifar da bala’i masifu kala-kala musamman kaci amanar wanda ya aminta da kai.

Shugaban buhari ya kwarewa wajen cin amanar wa’yanda suka aminta dashi ciki harda marayu talakawa makafi da Kuma abokan sa aminan sa na kusa-kusa.

Ubangiji mai girma da tsarki yana son ayi Gyara amma bashi bukatar tozarci ga ko wanne irin bil-adama shi Kuma shugaba buhari bashi da buri da ya wuce kamawa da tozartawa.

Shugaban buhari yaci amanar
Dr. Hakeem Baba-Ahmed wanda shine jami’in sa na hukumar zabe 2015 )Returning officer) wanda ya karbo Masa sakamakon zaben a hukumar zabe INEC Dr Hakeem Yasha barazana mai tarin yawa kafin zabe da Lokacin zabe har barzana akayi masa da cewa za’a saka masa bama-bamai amma ya jure ya daure duk domin shugaba buhari a tunanin sa da imanin sa shugaban buhari Mai adalci me Kuma ya zo ne da zuciyar Gyaran Nageriya da adalci ga talakawa daga karshe Bayan Dr Hakeem ya karbi sakamakon zaben buhari daga INEC ya Kai masa ko mukamin mai kwasar shara bai samu ba a karkashin Gwamnatin shugaba buhari.

Sanata Rabi’u musa kwankwaso shine Gwamna daya tal Kuma mafi daukar kasada Kuma shine jagoran kifar da Gwamnatin Goodluck Jonathan Wanda kowa ya sheda faruwar hakan Kwankwaso ya sha barazana har ta Kai ga an janye Masa tsaro daga karshe Kwankwaso sai kwaso ‘yan tauri yayi mafarauta ya jibge a gidan Gwamnatin jihar Kano domin su bashi tsaro.

Sanata Rabi’u Kwankwaso shine wanda yafi bawa shugaba buhari mafi tarin yawan kuri’a domin kuwa sai da ya bayarda kuri’u har kimanin kusan milyan biyu wato kuri’u 1,903,999 amma daga karshe buhari ko mutun daya bai iya dauka ya bawa aiki daga cikin tawagar yaran Sanata Rabi’u kwankwaso ba menene laifin kanawa da Kwankwaso?

Amma jihar lagos dake da kuri’u dubu dari bakwai da doriya 792,460
Tafi ko wacce jiha cin moriyar mulkin Buhari

Yaci amanar talakawa ‘yan Nageriya sama da mutun milyan dari da Suka aminta dashi.

Shugaba Muhammadu buhari yace yazo gyaran Nageriya ne amma sai ya fara Kama wa’yanda Suka fishi ilimi kudi da sanin makamar aiki Yana turawa zuwa gidan kurkuku, ya za’ayi su bar mulkinsa ya zauna lafiya?

Shugaba Muhammadu buhari ya rasa dattakun zama shugaba Babu Kuma wani shugaba a duniya da zaiyi nasara ba tare da dattaku ba.

Ire iren wannan matsaloli dake tare da Buhari yasa Gwamnatin sa ta gaza cimma Nasara daga karshe zai Gama mulki Babu daraja a idon shugabannin siyasa dana talakawa.

Bisa hasashen M inuwa MH:

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button