LABARAI/NEWS

BABU WANDA YAFI KARFIN JARRABAWA

BABU WANDA YAFI KARFIN JARRABAWA

Masu ganin cewa Maigirma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari bai hadu da jarrabawa na sharrin maciya amana ba sunyi kuskuren fahimta, gani suke hakan ba zai faru ba

Duk duniya babu wanda yafi karfin Allah Ya jarrabeshi, musamman shugaba wanda yake mulkin kasa hadin gambiza irin Nigeria da ta tattaro mutane masu banbancin addini, yare, kabila, tunani da manufa ya hadasu guri guda

Dole a samu munafukai da kuma masu cin amana a jikin Shugaba duk wanda yake kusancin da Gwamnatin Buhari ya san cewa akwai maciya amana a jikin Baba Buhari Maigaskiya, mu da muka yiwa wannan Gwamnatin hidima mun san da haka

Haka nan Allah Ya bamu labari a Qur’ani yadda munafukai maciya amana suka cutar da Manzon Rahama (SAW) har Allah Ya saukar da Surah mai sunan Munafukai Ya fayyacewa ManzonSa siffofin munafukai da suke zuwa jikinsa

Mu taimaki Shugaba Buhari da addu’ah, idan ya kubuta daga sharrin munafukai maciya amana tabbas zamu ga canji cikin gaggawa Muna rokon Allah Ya tona asirin maciya amana dake jikin Buhari idan sihiri suka masa Allah Ya karya sihirin Allah Ya nesanta tsakaninsa da su

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button