Videos

Bakori innanillahi yan bindiga sun kashe Mutum daya sun sace mutane shida a garin su jarumi lawan Ahmad

Inanillahi a kullum wannan harka ta rashin tsaro a Nigeria kara ɓaci take yau kaji wannan gobe kaji wannan gaba daya an kasa shwawo kan matsalar tsaro a wannan kasar wanda ko a kwanakin baya kunji mun kawo muku yadda ake kashe mutane a garin Katsina da kuma jihar Zamfara

Wannan ma dai akwai jarumi lawan Ahmad wanda yake shirya shirin izzar so wanda mutane sukafi sani da Umar Hashim kowa yasan badan jihar Kano bane dan jihar Katsina ne kuma wannan abinda ya faru acikin kyauye sune wanda ya fito yayi Allah wadai da wannan abin

An kashe mutum daya kuma an sace mutune shida wanda hakan ba karamar barazana bace ga mutanen wannan garin domin yanzu kowa zaina dar-dar da kansa akan wa’yannan yan bindiga

Jarumi lawan Ahmad yayi kira ga masu ƙarfin iko a wannan kasar domin suyi iya bakin kokarin su wajen kawo zaman lafiya a wannan garin dama masa baki daya

Jarumin an jiyoshi yana kuma yayi fadar wannan maganar saboda yadda abin ya kona masa rai Bama shiba hatta masu jin wannan labarin basuji dadin faruwar wannan abin ba

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button