LABARAI/NEWS

BAKU DA HUJJAR KARYATA ALAKARSA DA YAN KUNGIYAR OPC

BAKU DA HUJJAR KARYATA ALAKARSA DA YAN KUNGIYAR OPC

OPC na nufin Oduduwa People’s Congress wata kungiya ce ta ‘yan daba masu rike da manyan makaman yaki wanda suke fafutukar kafa Kasar Yarbawa zalla Oduduwa Republic kungiyar ta kafu a lokacin da Tinubu yake Gwamnan jihar Lagos

Yan OPC sun kaddamar da mugun harin ta’addanci akan Hausawa mazauna Lagos da nufin koransu gaba daya, sun kashe Hausawa dubbai, sun kwace biliyoyin Naira na Hausawa, sun raba matan aure da mazajensu, sun mayar da yara marayu, duk wannan abin ya faru akan idon Tinubu

A lokacin ne manyan Malamai irinsu shugaban shahidai a Nigeria Insha Allah marigayi Sheikh Ja’afar Kano suka yiwa Tinubu muganyar addu’ah tare da bada wasiyya mai tsauri akansa akan mimbarin juma’a saboda abinda ya bari ‘yan OPC suka yiwa Hausawa a Lagos bai hana ba saboda kabilanci

Amma yau an wayi gari an bawa wasu kwangila sun zo suna tallata mana wannan mutumin ba tare da sunyi la’akari da munanan manufofinsa ba, har suna karyata cewa Tinubu bai da alaka da ‘yan OPC, bashi ya kafasu ba

A wannan rubutun zan tabbatar da alakar Tinubu da ‘yan OPC, karatu ne ya biyo dani ta kan wani Littafi mai suna LEGAL AND FRAMEWORK OF PRIVATE SECURITY SERVICE IN NIGERIA wanda yake bayani akan tsarin dokoki da lasisin aikin hukumomin tsaro wanda ba na Gwamnati ba a Nigeria

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button