Islamic ChemistFadakarwaLABARAI/NEWSLatest Hausa Novels

BAMBANCIN GIRMAN BREAST TSAKANIN MATA

BAMBANCIN GIRMAN BREAST TSAKANIN MATA

Taswirar girma, zubi da tsari na Nonon Mace ya ta’allakane ga zubin jigidar halittar ta na gado (genetically) wanda shiyasa duk ƴan gida ko ƴan ɗaki ɗaya da wuya kaga ba irin zubin nonon su guda ba, zai wahala.

A nan ina magana ne akan Nono karan kansa. Bawai batun Nono ɗaya yafi ɗaya ba, wannan nasha faɗa is normal asami hakan ai ɗarin bawani significant bane can.


Saide a game da zubin duk nonuwan: Mu sani

  1. Yanayi na gado (Heriditary)
  2. Shekarun Mace (Age)
  3. Yanayin cimar da Mace ke samu (Nutrition)
  4. Adadin haihuwar datai
  5. Shayarwarta
  6. Samuwar Juna biyu da kuma,
  7. Yanayin yadda jiki ke samarwa da kuma sarrafa sinadarin estyrogin dake mamaye cigaban ƴan matantakarta

Duk waɗannan Abubuwan Bakwai ‘7’ kowanne ɗaya nada tasiri game da yadda zubin Nononta zai ko kuwa ya kasance.


▪️Haka zalik girman breast ka iya canzawa lokacin haila, ana iya ganin su qara tasowa saboda a lokacin estrogen ya hauhawa, don haka ana iya ganin haka a Mace ya zamto lokaci-lokaci kaga kamar breast din na caccanza wa.

▪️Hakama lokacin goyon ciki wato juna biyu girmansu kan ƙaru da kuma bayan haihuwa yayin shayarwa.

▪️Wani lokacin Zubin nada alaka ga ƙibar Mace da kuma yanayin motsawar sha’awa duk sukan canza.


🔴 Haka kuma cimar Mace, idan Mace bata samun isashshen abinci ko me inganci toh hakan zaisa jikinta yake qone kitsenta domin samar mata da kuzari kadda ta cutu, toh breasts shi kuma dama wadace yake da kitse (fats) wanda akarshe wannan fats din na daga wanda zai zaizaye domin hanta ta sami abinda zata samarwa mutum kuzari.

Kunga kenan shiyasa a masu ƙiba ma ake ganin suna dashi har yana neman fin karfin su tare da sanya su ciwon baya ko kafadu saboda excess fats. Shi yasa kuma Mace koda bata da ciki in kwai cima me kyau zata iya samun wadatattu.


🔴 Shayarwar bata zubar da nono abinda ke faruwa galibi shine yayi shayarwa dama ya bude duk bututun fitar nono sun bude toh bayan anyi yaye toh shine sukan Motse su koma yadda suke, shi kuma nonon sanda ya cicciko yayin shayarwa dama yai stretching fatar nonon shyasa sai aga kamar ya zube amma yadda yake haka yake. Saide wani abu guda a ƙarƙashin haka shine: in aka hada shayarwa da zama da yunwa toh kunsan nace jiki na qona fats don haka hakan zaisa aka sun qara zamowa kamar jaka sunyi qas saboda ruwa ya ɗauke kuma ɗan kitsen duk jiki ya konesa saboda babu diet.


🟡 Akwai kuma wanda haka kurum suke tun a halittar su sun sami matsala ko naqasun tsokokin dake haifar da girman nono wato hypoplasia kurum a zagwanye suke saboda babu tsokokin wadace sai yan kaɗan, irin wannan kan kasance da kananun nono kuma koda daga baya wajen shayarwa jariri kan fuskanci karancin nono, wasu kuma duk da kankantar nono still aga daya ya ɗan ɗara ɗaya, ko ya zamto kowanne ya ware gefe da gefe ansami fadin kirji a tsakaninsu.

Saide da yawa ba’a gane Mace nada hypoplastic breast sai bayan ta sami juna biyu ko haihuwa, domin ana iya ganinsu kanana amma juna biyu na samuwa kuma daga nan ainishin girmansu zai fara bayyana wanda daga nan kuma shikenan gaba sai mace ma tazo taji kamar tana neman kai dasu.

Haka still Mace ka iya kasancewa tana da kananun nonuwa kuma take samar da isashshen ruwan nono, duk normal ne.


Kananun nono bai nuna larura har sai ta tabbata na larurar ne, hakan kuma yasa duk wani maganin ƙarasu da za ai amfani dashi ba lallai kowacce inta yi ta sami hakan ba. Domin wasu nasu Heriditary ne.


Hakanan a likitance bamu da wani Maganin sa girman nono! Illa iyaka idan larura ce da tasa jikin Macen bai samar da sinadarin estrogen toh wannan munsan bama nono ba kwai sauran matsaloli da dama domin ko haila ma masu irin wannan kan kai shekara 18 basu ganta ba, sai an nemi daukin likita.


Amma baya ga wannan abinda likita kurum zai iya shine shawartar mutum ya rika ta’ammali da abinci ko abubuwa masu estrogen,

MISALI: Mata da yawa kan amfani da hulba (fanugreek) ko a likitance munsan tana da estrogen so bamu da case da hakan, saide ko yaushe tsaftace hannu ko abin shafawar, babu wani hatsari a likitance amma de kwai hatsarin mastitis inba a tsaftace komi ba, kada kwayoyin cuta su shiga kafar nono a sami rauni agun djn taɓa samun case irin hakan ta faru dalilin shafa man ko massage da ruwan saboda saka ci.

Ko shan madara ta waken suya, karas, fennel seeds, gyaɗa da sauran abubuwa masu estrogen.


Ko kuma final resort shine Breast Augmentation “SURGERY” Idan duk irin wancan recommendation ɗin bai samar da result ba. Wanda galibi dama inde irin nonuwan da ake karanta muku ne ko kuke gani a videon turawa toh dama LIFT ne.

Eh mana duk breast implant ne, Kuma ku tambayi kanku mana inda da akwai wani maganin asibiti na qara girman Nonuwa waɗannan porn stars ɗin, da celebrities ɗin dake cikin mawaƙa irinsu: Nicky, Kardashians, ds. babu abinda zai kaisu under the knife ana musu lift tare da qara CC Volume ɗin ana basu manyan breast ko kuma Butt Lift.

Wannan shine! so take it easy ƴan Mata, wani nonon sai bayan haihuwa, wani kuma haka kurum yake sai hakuri inde ba lift za ai miki ba. Karki bari depression ya kamaki.

┈┉┅━━┅┉┈┈┉┅━━┅┉┈

A ƁANGAREN MAZA

Haka dukkan Maza ya dace kusan wancan bayanin na sama kuma, domin kukan musgunawa Mata da ingiza Mata cikin garari iri-iri saboda kallon finafinan batsa da aka riƙa yi, da karatuttukan shafuka marasa inganci da sahihancin bayani dake karanta abu ba a yadda yake ba.

Haka kurum Mutum duk yazo ya tsani matarsa babu gaira babu dalili.

Wa ya gaya maka nonon ƴan porn natural nono ne? Duk asibiti suke zuwa mana, manyan kudaɗe suke biya ai musu Breast augmentation me kyau, In zaka iya biya aiwa Matarka shikenan.


Muna wata rayuwa ne da yanzu anfi fifita abunda ya bayyana wanda ido zai gani ya yaba ko yaji daɗi fiye dana ɓoye wato FAME (fem).

Mazaje yanzu basa shakkar kushe Matansu, ko kyararsu, ko kunyatasu ko kwatanta su da wata matar abokin su dalilin canzawar zubin jikinsu.

Don haka ko yaushe kake nazari kaga dawa kake tare? Wasu Matan tuni shekaru sun hau kansu, wasu kuma sun hayyafa ta inda bazai yiwu su taɓa komawa yadda ka santa daren farko ba.

Haka inka lura ai yanzu wasu ta haifo gasunan gabanku da yanzu suke nasu zamanin ƙila.


Tsanar Mace bayan ta fara kwana biyu ke nuna tun farko koda ba’a rigima tsakanin Mata da Mijin tode kwai alamun rashin fahimtar juna zama de kurum ake gashinan.

Idan kun fahimci juna toh duk yadda jikin Matarka ya canza sai kasan ya zakai ka farfado da wani abu dake baka gamsuwa da ita a duk yadda take, Ba kuma zaka wulakantata ba domin kaima kasan ba haka kake yanzu kamar baya ba.


Domin ni nasani kwai cikin Maza wadanda sam basu damu da kansu ba ballantana su kula, ƙazanta bakomi bace gani suke inde sun watsa ruwa shikenan alhalin hatta wankan sun mance cewa shima iyawa ne. Ballantana azo tsaftar al’aura da sauransu, kai ka damu da breast amma zahiri ita kukan zuci take duk sanda ka nemeta, kurum biyayyar aure take amma bata jin komi dakai.

Me kokarin gaske ce ma ke nuna kamar tanajin daɗin wani abu don karka tsargu musamman inkana kyautata mata.


Sai de ta wani ɓangaren duk da hakan, baya ga kallon surar kirjin wasu Matan da mazan keyi suji nasun sun gaza… Ku kanku Matan kune ke buɗe kofar hakan lokutan da dama, Mata da kanku ke zubar da Mutuncin Mata ƴan uwanku, tare da wulakanta junanku ta hanyar rubuce rubucenku.

Inka duba youtube duk wani video dake bayanin jima’i ko rubutaccen novel na fitsara zaka ga Matan ne Authors, suke rubutawa ko ɗora videon ba Maza ba. Ba ruwan Maza da wannan aikin, na kuma ƙalubalanci duk me ja akan hakan.

Don haka please mui hakuri da juna, wani abun hakuri ake ba bukatar sai an korafi, a duk rayuwar guda nawa ce? sai saura.

✍🏻
[Ibrahim Y. Yusuf]

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button