Daga Malaman mu

Bari Mubaku Wani Dan Darasi:

Bari Mubaku Wani Dan Darasi:

Cewa inason ka, ko ina sonki baya nufin aure ko saduwa tsakanin mutum biyu.

Duk wanda kakeso ce kanason shi, hausawan mu ne ke ganin kalmar da nauyi kace kanason masoyinka.

A zahirin gaske kuma (Halal ne) kace kanason Babanka, mamar ka, abokinka, abokiyarka, abokiyarki, kanwarka, kanwarki, kanin ka, kanin ki, matar ka, mijin ki, da duk wani wanda kakeso. Matukar ba kafiri bane.

⬆️⬆️ Say it loudly.

Yanda soyayya ke tabbata:

Na daya yazama dole a kiyaye dokokin Allah.

Na biyu kyautatawa tsakanin juna ta hanyar taimakon kudi, shawari nagari, kamalai masu sanyi, kishin juna da kyakkyawan fata ga juna.

Idan akayi haka to ko bayan ansamu rabuwa za’ayita tunanin juna da neman sake haduwa. Amma idan akayi akasin haka, bayan ansamu rabuwa za’a zage juna da cin mutuncin juna, da yiwa juna kazafi ga juna, da karya da bala’i.

Allah ya kyauta.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button