LABARAI/NEWS

BARI NA WARWARE MUKU GASKIYA MATA

BARI NA WARWARE MUKU GASKIYA MATA
🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍

Inde kin yadda ke Macece kin kuma yadda da kanki kina da lafiya, tsafta da kamala toh kurum kece.

Wadannan abubuwan da wasu cikin Mata ke hura hanci dasu koma wasu cikin Maza ke wahal da kansu kan sai Mace mai abu kaza da kaza ina mai tabbatar muku mude a ilmance a halittance kuma a likitance babu wani ɓoyayyen tasiri na abu daban da Mace mai su tafi yar uwarta Mace.

Ya kamata ku tausayawa kanku ku dena sanya kanku a wahala, kubar zukatanku su huta. Ba Macen da bayyanar wata suffa jikinta ke nuna tafi wata a shimf…..ɗa. Duk Mace kurum Mace ce saide in ansami larura.

Kurum de dake kunsan kwakwalwa ke sarrafa komi, kuma kowanne da yadda yake ganin kyawu, abinda zai ɗau hankalin wani a wajen wani ko ɗaga kai ya kalli abin saide in ya zama dole amma bazai ba. Don haka inkai kana kallon Mace me wata suffa cewa taimaka a shimfiɗa toh karka ce kowa ma yaje ya kwashi irinta, kuskure ne.

■ DIMPLES: Nai muku bayanin dalilinsa cewa naqasa ce dakan zamo ribar kyau ga wasu sakamakon wata tsoka da bata kai tsayin ta ba wanda shi yasa ake samun kwarmin don haka me ya haɗa dimples da dadin jima’i? Kurum de fuskarce inka sawa ranka toh

■ GAP TEEH: Yana faruwa ne idan ya zamto mukamikin mutum babba ne amma hakoransa sun zamo ƙanana akan ƙashin muƙamikin. Don haka akan muƙamikin ne haƙoran suke ƙanana bawai yadda muke ganinsu da ido ba shine ake samun tazarar musamman hakoran tsakiya saboda kan bend (wato lanƙwasar ƙashin muƙamikin suke)…

Wani lokacin kuma kan faru ne idan hakori ya fita kuma ya zamto sannan hakorin da ake KIRA WISDOM TEEH bai fito ba toh in wisdom ya fito sai ya zamto ya turo sauran hakoran sun harhade inda daga baya inda wancan haƙorin incisors ya fita sai ya zamo Gap.. ake ganin ga space amma bai kai na girman hakori ba. Don haka menene hadinsa da farji ko daɗin kwanciya?

■ NECK WRINKLES: Galibi inba wacce ta fara tsufa ba toh sai mace mai jiki ko mai kiba dama ake ganinsa… kamar yadda kitse yake hawa kusan hudu ajikin mutum kowanne da zubinsa… don haka dama suna da ƙiba giɓin masu shi, ko ince kaurarane kuma duk Mata dama kitsene kwance kasan fatarsu wanda shike basu laushin jiki ko ya ka taɓasu… shine kuma yasa lokacin zafi suka fi kowa jinsa…

Toh shi wannan kitsen “loose fat” mai laushi sakamakon kibar macen sai yasa fatarta bazata iya stretching ta mike straight ba… saboda kwanciyar fats din yasa ba space don haka saitai loose yaci gaba da kwanciya sai ya haifar da wannan GURUN na wuya. Don haka me ya hadashi da jima’i? cikin fararen fata ma inkaga takaicin dake kamasu dalilin sa zakui mamaki tashi tsaye suke da exercise da shafa magunguna har sai ya ɓace… saide inba yadda zasui. Maimakon haka gara kace Mace me ƙiba kai tafi baka gamsashshen jima’i amma ba guru ba, wani kuma mara kibar tafi bashi.

Don haka ƙila gurin ne kai ke motsa ma sha’awa, kamar yadda kowa nada abinda shi yafi ɗaukar hankalinsa a jikin Mace, dama Allah bai yi mu ɗaya ba.

┈┉┅━━┅┉┈┈┉┅━━┅┉┈

Don haka adunkule wadannan abubuwa basu da alaka da jima’i. Ba daidai bane kina Mace ki matsawa kanki cewa ke baki da kaza irin na wance, ko kuwa Maza duk sunfi son kaza… Alhalin ke kanki aranki ba son abin kike ba, kurum de don surutu ne. Mata nawa ne basu damu da manyan nonuwa ba da zasu iya rage nasu da sun rage, wasu kuma da kudi ido bude nema suke.

Don haka ki yarda da kanki ba a fiki ba, lla iyaka abinda wasu sukafi sauran Mata shine abin de da kuke iya gani da idonku wato suna dashi baku dashi… idan abin na baka sha’awa toh shine de ke baka sha’awar, karka kuskura ka debi Mace akan wani yace ma me suffa kaza tana daɗin kaza, kafi kowa sanin kanka, kaine zaka saurari kanka akan me kake so, Amma inka bi ra’ayin wani wai ai me kaza tafi sauran Mata daɗin kwanciya ina mai tabbatar maka zaka sami matsala, za kuma kaji haushin kanka.

Idan abu yana burgeka da Mace bisa ra’ayin kanka toh shikenan haka akeso dama ace Mace na birge mijinta.

Amma karka ɗebeta da wata manufa daban. Ita kwanciya iyawane kurum abubuwan basa wuce 6 dake maida kowacce Mace kwararriya ahakan… bawai ajika abun yake ba, Aa’h a hikimarta ne.

Don haka ku dena sama kanku depression duk Mace toh Mace ce kurum. Akula da tsafta, a iya magana, arika samun isashshen bacci, arika shan ruwa sosai, arika cin fruits, arika brush, da murmushi… wannan sune ke daɗa fifita lafiyar Mace…. sauran batun kuma ahannunta da kuma dabararta yake.

Ku dena jin kaskanci… duk kuma Matane.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button