ylliX - Online Advertising Network Bayan Bidiyon Dollar Babu Wani Labari Da Ya Ɗauki Hankalin Ƙasashen Turai Da Ya Shafi Ganduje Kamar Labarin Gurfanar Da UniquePikin, Cewar Barista Abba Hikima - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Bayan Bidiyon Dollar Babu Wani Labari Da Ya Ɗauki Hankalin Ƙasashen Turai Da Ya Shafi Ganduje Kamar Labarin Gurfanar Da UniquePikin, Cewar Barista Abba Hikima

Bayan Bidiyon Dollar Babu Wani Labari Da Ya Ɗauki Hankalin Ƙasashen Turai Da Ya Shafi Ganduje Kamar Labarin Gurfanar Da UniquePikin, Cewar Barista Abba Hikima

Bayan videon dollar babu wani labari da ya dauki hankalin kafafen yada labaran Kasashen Turai da ya shafi Ganduje kamar labarin gurfanar da su UniquePikin. CNN, BBC, Aljazeera, DW da sauran su sun dauki labarin kuma sun kambama abun.

Duk wanda ma bai ga vidion da yaran suka yi ba da yanzu ya gani. Kuma turawan da muke neman yardar su sun yiwa gwamnatin Gandujen bakin fenti. Shi yasa nace muku Zai yi wuya Gwamnatin Ganduje ta kara hukunta wani yaro akan irin wannan.

 

 

Ba don ina goyon bayan shugabanni ba kamar tun a rubutu na na fada. A’a
saboda dimukradyya kuka ce kuna yi. Kuma hukuncin da aka yiwa wannan yara ba na shariar Musulunci bane. Na Penal Code ne. Saboda haka dole idan za’a yi sharhi a yishi a dimukradiyance.

A Shariar Musulunci bata suna wanda ake kira Kazafi ne kawai hukuncin sa yazo karara a Qurani da Sunnah. Shine ka bata wa mutum suna da yin zina ko neman maza. Hukuncin sa shine Bulala k80. Duk bata sunan da ba wannan ba sai dai a duba a gani civil ne ko criminal. Sannar Ta’azir za ayi ko Diyya za a sa a biya da sauran su.

Kuma ina maimaitawa, abun da ya fiyewa shugabanni musamman na siyasa shine suyi hakuri idan an taba su. Idan basu yi ba. To zasu jawa kan su abunda za suyi da na sani.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button