LABARAI/NEWS

Bayanin Aminu Saira Kan Canja Nafisa Abdullahi Zuwa Fati Washa

Bayanin Aminu Saira Kan Canja Nafisa Abdullahi Zuwa Fati Washa

Aminu Saira Yayi Bayani Kan Canja Jaruma Nafisa Abdullahi Zuwa Fati Washa A Shirin LABARINA Series! Anyi Takaitaccen Hira Da Mashiryin Shirin Na LABARINA Kan Yadda Ake Canja Jarumi Idan Ana Tsaka Da Series Kamar Yadda Akaga Sauye Sauyen Fuskoki A Cikin Shirin Nasu.

Idan Baku Manta Ba A Kwanakin Baya Ne Aka Samu Tsaiko A Wannan Shirin Inda Wasu Jarumai Jiga Jigai Su Sanar Da Fitarsu Daga Shirin. Hakan Ne Ya Damama Shirin Lissafi, Daga Bisani Kuma Sai Labarin Shirin Ya Fara Sauyawa.

Tun Farko Dai Jarumi Nuhu Abdullahi (Mahmud) Shine Wanda Ya Fara Ficewa Daga Shirin, Inda Aka Bayyana Mahmud A Matsayin Cewa Ya Mutu, Sai Kuma Maryam Wazeery (Laila) Wacce Tayi Aure Ita Kuma A Bayyana Cewa Ta Bar Kasar Kwata Kwata.

Daga Bisani Asalin Jigon Tafiyar Shirin Wato Nafisa Abdullahi (Sumayya) Ta Sanar Da Ficewarta Daga Shirin, Daga Nan Ne Kum Shirin Ya Fara Samun Babban Kalubale, Labarin Ya Zama Yana Tangaltangal. Hakan Ne Yasa Mashiryin Shirin Malam Aminu Saira Saura Tunani Domin Maye Gurbin Ita Nafisa Abdullahi (Sumayya) Zuwa Wata Sabuwar Fuska.

Sakamakon Wannan Gurbi Dole Ne A Cikeshi Idan Har Anaso Shirin Na LABARINA Ya Dawo Da Armashinsa. Cikin Satin Nan Ne Akaga Wani Gajeran Bidiyo Da Yake Nuna Kamar Fati Washa Itace Ta Maye Gurbin Sumayya A Cikin Shirin.

Kalla Bidiyon Nan Domin Samun Karin Bayani. Da Kuma Shirar Da Akayi Da Malam Aminu Saira.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button