LABARAI/NEWS

Bello turji ya nemi afuwa a yafe masa Ni Mutumin Kirki Ne Sallah Ba Ta Wuce Ni A Kan Lokaci Cewar Bello Turji

Bello turji ya nemi afuwa a yafe masa Ni Mutumin Kirki Ne Sallah Ba Ta Wuce Ni A Kan Lokaci Cewar Bello Turji

Fitaccen Danta’adda a Najeriya wanda ya yi kaurin suna wajen kashe mutane da garkuwa da su a dazukan da ke tsakanin jihar Zamafa da Sokoto wato Bello Turji ya bayyana cewa shi cikakken musulmi ne kuma sallah ba ta wuce shi a kan lokaci

A yayin zantawarsa da kamfanin watsa labarai na Aminiya Bello Turji ya kalubalanci masu zargin sa da yi wa ‘yan mata fyade, zargin da ya ce sam babu gaskiya a cikinsa

Sannan kuma ya yi maganar ba mu bin addini ai ba nasa ba ne na Allahn da ya halicce mu ne, ko mun yi bai ganewa Sannan maganar da nake yanzu ai a masallaci ka iske ni kuma sallah na yi wa mahaliccina ba kaina na yi wa ba saboda ina gudun haduwata da shi

Bello Yabo karya yake da ya ce wai ya zauna da ni a Kurkuku. Karya yake idan ma Malami ne na gaske ko bai taba yi wa kowa karya ba, ni sai Allah ya isar min saboda ban taba zuwa Kurkuku ba

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button