LABARAI/NEWS

Bello Turji Ya Sake Tsallake Rijiya Da Baya A Harin Sojojin Sama

Bello Turji Ya Sake Tsallake Rijiya Da Baya A Harin Sojojin Sama
Samakon harin da Sojojin sama suka kai masa

A safiyar yau Litinin 19 ga watan Satumbar 2022 ne jirgin sojojin saman Najeriya ya sake kai mummunan hari kan maɓoyar riƙaƙƙen ɗan bindigar nan, Bello Turji a jihar Zamfara

yadda Bello Turjin ya tsallake rijiya da baya yayin wani harin da sojojin suka kai masa a gidansa ranar Asabar Wata majiya daga yankin ta shaida wa Aminiya cewa jirgin yakin ya sake dawowa da safiyar ta Litinin, inda ya jefa bama-bamai akalla guda biyu, da wajen misalin karfe 9:00 na safe

A wani labarin kuma wasu ’yan bindiga da ake zargin yaran Turjin ne sun kaddamar da hari kan matafiya a kan hanyar Sakkwato zuwa Gusau, a daidai garin Shinkafi na jihar Zamfara da safiyar Litinin

Wani mazaunin yankin na Shinkafi, Murtala Wadatau, ya ce maharan sun tare hanyar ne a daidai garuruwan Kwanar Badarawa da Birnin Yero

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button