LABARAI/NEWS

Bidiyon barayi 2 da bacci ya sace bayan sun yashe dakin wata tsohuwa

Bidiyon barayi 2 da bacci ya sace bayan sun yashe dakin wata tsohuwa

Wani abin al’ajabi ya auku a gidan wata tsohuwa da ke Hammanskraal a Pretoria cikin kasar Afirka ta kudu inda bacci ya kwashe wasu barayi biyu bayan sun gama tafka sata, LIB ta ruwaito.

An samu bayanai akan yadda barayin suka balle kofar gidan matar a ranar Alhamis din da ta gabata, 14 ga watan Afirilu inda suka sace talabijin din bango, na’urar microwave, takalma da sauran abubuwa.

Sai dai yayin da suke kokarin fita gidan ne abin mamaki ya auku, don take anan bacci ya kwashe su.

Ga hotuna da bidiyon su kwance shane-shane suna bacci a kasa:

https://www.instagram.com/p/CckeEXKNXxz/?utm_source=ig_web_copy_link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button