Latest Hausa NovelsLABARAI/NEWS

Bidiyon Safara’u ta Kwana Casa’in tana tikar rawa da wakarta ta ‘Kwalelenka’ maza su na mata manni bayan an cire ta a fim

Bidiyon Safara’u ta Kwana Casa’in tana tikar rawa da wakarta ta ‘Kwalelenka’ maza su na mata manni bayan an cire ta a fim

Yadda Safara’u ta Kwana Casa’in ta koma tara maza tana rawa da waka su na mata manni bayan an cire ta a fim

Jaruma Safeeya Yusuf wacce aka fi sani da Safara’u ta shirin fim mai dogon zango na Kwana Casa’in tana shan caccaka ta ko ina bayan ta bar fim din inda ta koma yin waka.

Kamar yadda cikin kwanakin nan bidiyonta ya dinga yawo a kafar sada zumunta wanda ta hau kan wata wakarta mai suna “Kwalelenka”, kowa ya razana.

Mutane da dama sun dinga yi mata fatan shiriya tare da neman iyayenta ko kuma wasu da ke da iko da ita da su yi gaggawar dakatar da ita daga turbar da ta dauka.

Sai dai a jiya, ranar Laraba ta saki wasu bidiyoyinta da wata shiga ta kananun kaya tana rawa da waka bayan ta tara maza a wani wuri mai kama da shagalin sallah.

A bidiyon ta hau wakar ta ta mai suna “Kwalelenka wacce mazan su ka dinga yi mata amshi tare da lika mata kudade.

Nan da nan mutane su ka tafi karkashin bidiyon su ka dinga yi mata fatan shiriya har da masu cewa ta zama abin tausayi don wannan hanyar da ta dauka ba mai kyau bace.

A cikin wakar an ji baitin da ta ke cewa “na bar sana’ar wa ‘yan wahala”, da alamu ta hassala ne bayan cire ta daga fim, hakan ya sa ta ke yi wa ‘yan Kannywood habaici.

Ga bidiyon wanda ta sanya a shafinta:

https://www.instagram.com/reel/CdJzOL-Fkxj/?utm_source=ig_web_copy_link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button