Birthday din Murja kunu ya janyo Cece kuce / A’isha najamu na shan suka da zagi

Bikin taya Murja shaharriyar yar TikTok din arewa ya janyo Cece kuce biyo bayan yadda bikin ya kayatu
An dai gudanar da bikin taya ta murnar ranar zagayowar shekarar haihuwar ta ne inda mutane da dama suka taya ta tare da yi ma ta addu’a da dama
Murja wacce ta kasance fitacciya ce a Kafar TikTok na cigaba da nuna jin dadin ta kan yadda mutane da dama suka taya ta tare da aike ma ta sako
Duk da kasancewar ta rigimammiya da kuka ta janyo fada hadi da Cece kuce a kafafen sada zumunta hakan bai hana mutane aike ma ta da sako ba
Wani abun mamaki shine yadda aka janyo babbar abokiyar rigimar ta , A’isha najamu watoh A’isha izzar so ta aike ma ta da sako duk da kasancewa kwai tsamin Alaqa a tsakanin su
Bikin dai ya matukar kayatu lamarin da ya janyo Cece kuce hadi da janyo magangan a shafukan sada zumunta