LABARAI/NEWSFadakarwa

BOYAYYEN AL’AMARIN DAKAN FARU CIKIN CIYAR DA MABUKATA MUSAMMAN A RAMADAN

BOYAYYEN AL’AMARIN DAKAN FARU CIKIN CIYAR DA MABUKATA MUSAMMAN A RAMADAN

A wajen ciyar da mai azumi daya a wuni daya, zai iya yiwa ka samu lada fiye da wanda zaka samu a azuminka daga farkon watan Ramadan zuwa karshensa, sabanin yadda muka sani na samun ladan azumin wannan yinin na wanda ka ciyar. Domin akwai bayin Allah masu taqawa da tsoron Allah wanda ibadunsu keda matukar nauyi akan mizani duk da suna raye cikin kangin talauci.

Suna kwana su wuni wajen bautar Allah (SWT) bisa ikhlasi. Wasu daga cikin irin wadannan bayin Allah suna nan bayyane kamar yadda zamu iya kyautata masu zato, wasu kuma Allah ya boye shi kadai ya barwa kansa saninsu. Domin wani darajarsa bama a ibada take ba, A’a zaka samune anjarabcesa da babu amma duk da haka baya kwana kullace da kowa cikin ransa.

Daraja da ladan azumi daya na irin wannan bayin Allah ta zarta tawa da taka nikin- baninki. Shiyasa Allah yace irin wadannan mutane ko rantsuwa sukai cewa gobe ko yau za’ai ruwa toh ko banyi niyyar yin ruwan ba saina sauko da yayyafi me karfi don kar sui kaffara

To idan Allah ya yi mana gam-da-katar muka ciyar da irin wadannan bayin Allah lokacin azumi, Allah zai bamu kwatankwacin ladansu, da darajarsa, da kimarsa batare da an tauye komai ba, sannan kuma ga ladar namu azumin. Ka daure ka ciyar dasu abinci sosai bawai kurum ka basu dabino kunu ko koko ba. Inkana da hali basu abunda zasu dafa suci su koshi har azumin ya wuce.

Allah ka bamu ikon ciyar da halal akan tafarkinka bisa ikhlasi amin.

KUNGA WANNAN HOTON NA KASA AKWAI SOSA RAI GA DUK MAI IMANI

Karshenta yana da yaya 2 ko 1 amma da yawan mu basu da hankali zaka samu mutum jira yake sai ubansa ya rokesa, wani yana gani anacin abinci agida kullum amma dan uban nada dan hali ya dauka shikenan akan me shi zai sayo abinci aci, kaga wawan tunani fa!.

Don haka nide don Allah alumma wlh irin wadannan dattijan da yawa muna da halin saye baki daya kayan jarin da irin wadannan mutanen ke kasawa da sunan sayarwa, wani duk kayan basufi dari 400 ba wlh, wani 350. Ahaka zai sayar yaje yaci da iyali.

Mu daure mu karfafesu ta hanyar saye inda hali ma mu ninka musu kudin, gobe sai kaga sun karo yawansu ana haka kan ka ankara shikenan ko ance suje sui bara bazasui ba domin sungane sana’ar tafi musu kima.

Yanzu ka dubi kayan gabansa da iska zatazo tsaf zata kwashe tai gaba tare da watsi dasu, kuma wlh da zaka riskeshi sanda iskar ta kwashe kayan murmushi zaka ga yanayi. duk da cikin ransa yasan asarace ta sameshi, toh amma saboda juriya da gogayya arayuwa shiyasa karamar kyauta garesu saita sasu kukan dadi tare da fidda hawaye maimakon yinsa sanda asara ta samesu.

Allah ka bamu ikon kula da iyayen mu, ka tsaremu da shiga halin Qaqanikayi mu dasu baki daya amin.

Karmu manta mu yawaita fadin HASBUNALLAHU WA NI’IMAL WAKIL

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button