LABARAI/NEWS

Budurwar Ta Kai Kanta Ga Ƴan Sanda Bayan Saurayin Ta Ɗan Ƙasar Turkiyya Na Neman Ta Ruwa A Jallo

Budurwar Ta Kai Kanta Ga Ƴan Sanda Bayan Saurayin Ta Ɗan Ƙasar Turkiyya Na Neman Ta Ruwa A Jallo wata budurwa ta miƙa kanta ga rundunar ƴan sandan jihar biyo bayan neman da saurayin ta ɗan ƙasar Turkiyya ke yi ruwa a jallo

Nasir Zango bai yi wani ƙarin haske kan lamarin ba kuma zuwa yanzu babu wata hukuma data tabbatar da afkuwar lamarin Wannan na zuwa ne yayin da wata kotu ta aike da ɗan ƙasar Chinan nan da ake zargin ya kashe tsohuwar budurwar Ummita Kurkuku bayan bayan kisan da ya yi mata kwanaki biyar da suka gabata.

Kungiyar Sinawa yan kasuwa a Najeriya ta yi alla-wadai da kisan da ake zargin Mr Quanrong ya yi wa Ummita Da take mika sakon ta’aziyya ga iyayenta kungiyar ta ce tana ba da cikakken goyon baya ga doka ta yi aikin ta

A cikin sanarwar da ta fitar kungiyar ta ce abin da ake zargin Mr Quanrong ya aikata abin alla-wadai ne kuma babban laifi ne da ya kamata a bar hukumomin tsaro su yi aiki don tabbatar da abin da ya faru

Mahaifiyar Ummita Hajiya Lami Sani Buhari ta ce mutumin da ake zargi da kashe ‘yarta ya sha zuwa gidansu yana neman ganin Ummita amma ba ta son fitowa sai ranar ne Allah ya bashi Sa’a ya shigo gidan

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button