LABARAI/NEWS

Budurwar Ta Kai Kanta Ga Ƴan Sanda Ne Bayan Saurayin Ta Ɗan Ƙasar Turkiyya Na Neman Ta Ruwa A Jallo

Budurwar Ta Kai Kanta Ga Ƴan Sanda Ne Bayan Saurayin Ta Ɗan Ƙasar Turkiyya Na Neman Ta Ruwa A Jallo

Rahotanni daga jihar Kano a Arewacin Najeriya, na cewa wata budurwa ta miƙa kanta ga rundunar ƴan sandan jihar biyo bayan neman da saurayin ta ɗan ƙasar Turkiyya ke yi ruwa a jallo

Cikin wani saƙo da ɗan jarida Nazir Salisu Zango ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Laraba, ya ce wata budurwa ta miƙa kanta ga ‘yansanda a Kano bayan da wani saurayin ta dan ƙasar Turkiyya ke neman ta ruwa a Jallo

Nasir Zango bai yi wani ƙarin haske kan lamarin ba, kuma zuwa yanzu babu wata hukuma data tabbatar da afkuwar lamarin

Wannan na zuwa ne yayin da wata kotu ta aike da ɗan ƙasar Chinan nan da ake zargin ya kashe tsohuwar budurwar Ummita Kurkuku, bayan bayan kisan da ya yi mata kwanaki biyar da suka gabata.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button