LABARAI/NEWS
Buhari ya sanar da hanyar da yake so a bi wurin zaban ɗan takarar shugaban ƙasa na APC

Buhari ya sanar da hanyar da yake so a bi wurin zaban ɗan takarar shugaban ƙasa na APC
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari bayan ganawa da gwamnonin jihohin APC, ya bayyana cewa zaɓen fidda ɗan takaran shugaban ƙasa na jam’iyyar APC za’a gudanar da shi ne bisa tsarin wakilan jam’iyya “delegate” ba maslaha ba wato “Consensus”.
Tuni dai jamiyyar APC ta ƙasa ta fitar da adadin wakilai “delegates” da za su yi zaben ɗan takarar Shugaban ƙasa a ko wanne yanki a faɗin Najeriya.
1- Kudu maso Gabas — 288
2- Kudu maso Yamma — 411
3- Kudu maso Kudu — 359
4- Arewa maso Yamma — 558
5- Arewa ta Tsakiya — 363
6- Arewa maso Gabas — 336
Arewacin Najeriya — 1,257
Kudancin Najeriya — 1,068