LABARAI/NEWS

Buhari Ya Umarci Manyan Hafshoshin Soji Da Su Koma Yankin Arewa Maso Gabas.

Buhari Ya Umarci Manyan Hafshoshin Soji Da Su Koma Yankin Arewa Maso Gabas.

Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci manyan hafshoshin sojin kasar nan da su koma yankin Arewa Maso Gabas don taimaka wa nasarorin da dakarun soji suka samar na yakar ‘yan ta’adda a yankin da a sauran sassa.

Buhari ya bayar da wannan umarnin ne a NDA da ke Jihar Kaduna a taron yaye wa da kuma kaddamar da daukar sabbin dalibai na karo 69 da suka hada da na sama da na kasa

A cikin sanarwar da mai magana da da yawun fadar shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya fitar, Buhari ya ce, Na umarci manyan hafshoshin sojin kasar da su tare a yankin Arewa Maso Gabas domin dora wa a kan nasarorin da aka samu na yakar ta’addanci a yankin, ina kuma kira ga ‘yan Nijeriya su ci gaba da ba bai wa jami’an tsaro na soji da sauran jami’an tsaro goyon baya domin a samu nasarar kawar da ta’addanci a daukacin fadin kasar nan

Yin hakan na da muhimmanci matuka, musamman ganin cewa zaben 2023 na kara karatowa, na kuma daukar wa kaina alkawarin tabbatar da an gudanar da zabubbuka cikin kwanciyar hankali da lumana da kuma tabbatar da an gudanar da sahihin kuma ingantaccen zabe, wannan duk nauyi ne da ya rataya a wuyan kowanne dan Nijeriya

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button