ylliX - Online Advertising Network cin amanar aikin soja da tsaron kasa - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

cin amanar aikin soja da tsaron kasa

CIN AMANAR AIKIN SOJI DA TSARON KASA

Jami’an yan sanda sun kama wani gurbataccen soja mai suna Nafiu wanda yake aiki a rundinar Muhammadu Buhari Cantonment birnin tarayya Abuja bisa zargin yana sayar da bindigogi da harsashi wa ‘yan ta’adda masu garkuwa da mutane.

Bayan sayar da bindigogi da sojan mai mukamin Kofur yake yi wa ‘yan ta’adda sannan kuma yana basu hayar bindigogi yana bada hayar kowace bindiga wa masu garkuwa da mutane akan kudi Naira dubu dari uku (300,000) a operation daya.

Yadda jami’an ‘yan sandan farin kaya suka kamashi shine an kama wasu masu garkuwa da mutane ne a Abuja sai aka tambayesu a ina suke samun bindiga da suke operation sai suka ambaci sunan wannan soja, to shine sai aka sa su kirashi domin ya sake kawo bindiga a wani sabon operation.

To ya dauko wannan sabuwar bindiga a cikin motarsa kirar AK47 cike da harsashi da kuke gani a bidiyo zai kawo ya sayar da ita akan kudi Naira Miliyan 3 ba tare da ya fahimci tarko aka dana masa ba yana zuwa sai jami’an tsaro suka cafke shi

Gashi nan dai ya fara nadama marar amfani, haka al’amarin cin amana yake, duk wanda yaci amana sai amanata ta ci shi komin daren dadewaMuna rokon Allah Ya cigaba da tona asirin maciya amanar tsaron Nigeria

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button