ylliX - Online Advertising Network Da Ɗumi Ɗuminsa: An Aike Da MR 442 Gidan Maza A Jamhuriyar Nijar - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Da Ɗumi Ɗuminsa: An Aike Da MR 442 Gidan Maza A Jamhuriyar Nijar

Da Ɗumi Ɗuminsa: An Aike Da MR 442 Gidan Maza A Jamhuriyar Nijar

Fitaccen mawakin Hipop dinnan wanda aka fi sani da Mr_442 tare da abokin aikin sa Ola Of Kano, sun hadu da fushin hukuma a jamhuriyar Nijer bayan da suks aikata laifi mai girma.

Jaridar Amintacciya ta rawaito cewa, Ɗaya daga cikin makusantan mawakin Murja Ibrahim Kunya ce, ta bayyana haka a shafin ta na TikTok.

 

Murja ta bayyana cewa tuni an aike da Mr 442 da abokin aikin shi zuwa gidan gyaran hali a Jamhuriyar Nijar tare da Tarar aƙalla Naira Milyan Goma kowannen su.

Murja ta bayyana irin laifin da sukayi inda tace, tunda farko mawakan sunyi yunkurin yin International passport ne a Jamhuriyar Nijer, lamarin da ya zama babban laifi ga duk wanda ba dan kasar ba.

Mawakan biyu sunyi yunkurin yinsa ne, da niyyar samun damar haurawa kasashe da dama, dukda sun san cewa hakan babban laifi ne, inda suka yi aski da niyyar gujewa lamarin don kada a gane su yayin, yin passport din, sai dai kasancewar su sanannu hakan yasa aka gane su tare da kamasu.

Bayan da aka gano su an kama mawakan tare da kaisu gidan yari, wata majiya ta bayyana mana cewa wannan abinda sukai laifi ne babba a Nijar wanda zai iya sawa ayi musu hukuncin shekaru 6 kowanne a gidan yari.

Idan dai ba’a manta ba Mr 442 ya shahara ne a Kafafen watsa labarai tun bayan haɗuwar su da Safara’u ta cikin shirin gidan Kwana chas’in wato Safaa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button