ylliX - Online Advertising Network DA DUMI DUMI: ASUU Ta Dakatar Da Yajin Aiki Da Ta Dauki Watanni 8 Tanayi Bisa Sharadi - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

DA DUMI DUMI: ASUU Ta Dakatar Da Yajin Aiki Da Ta Dauki Watanni 8 Tanayi Bisa Sharadi

DA DUMI DUMI: ASUU Ta Dakatar Da Yajin Aiki Da Ta Dauki Watanni 8 Tanayi Bisa Sharadi.

Kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta dakatar da yajin aikinta na tsawon watanni takwas bisa sharadi.

Kungiyar ta yanke shawarar dakatar da yajin aikin ne a wani taron shugabanninta da aka fara tun a daren ranar Alhamis wanda ya kai a safiyar Juma’a.

Kungiyar ta kira taron ne domin sanin matakin da za ta dauka na gaba bayan da rassanta na jihohin kasar suka gana kan hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke a makon jiya.

Kotun daukaka kara ta umurci ASUU da ta dakatar da yajin aikin kafin a saurari karar da ta daukaka kan hukuncin da ta umarci malaman da su koma bakin aiki.

Mambobin kwamitin zartaswa na kungiyar na kasa, wadanda suka hada da shugabannin kungiyoyin na kasa da kasa, sun halarci taron a sakatariyar ASUU ta kasa da ke Abuja.

ASUU dai ta shiga yajin aikin ne tun ranar 14 ga watan Fabrairun bana.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button