ylliX - Online Advertising Network DA DUMI-DUMI: Babu maganar cire rubutun Ajami daga jikin naira, mun tattauna da gwamnan banki - Sarki Sanusi ya fadawa malaman Najeriya - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

DA DUMI-DUMI: Babu maganar cire rubutun Ajami daga jikin naira, mun tattauna da gwamnan banki – Sarki Sanusi ya fadawa malaman Najeriya

DA DUMI-DUMI: Babu maganar cire rubutun Ajami daga jikin naira, mun tattauna da gwamnan banki – Sarki Sanusi ya fadawa malaman Najeriya

Shugaban darikar Tijjaniyya a Najeriya, Mai Martaba Sunusi Lamido Sunusi, ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa su kwantar da hankalinsu, domin batun cire rubutun Ajami jita-jita ce kawai.

Hakazalika Sarkin ya ce bayan jin wannan batu sai ya kira gwamnan babban bankin kasa ta wayar tarho domin jin gaskiyar lamarin, gwamnan ya shaida masa cewa babu maganar cire Ajami

Sai dai sarkin ya je ya zauna da gwamnan domin samun gamsasshiyar hujja domin da yawa daga cikin malamai suna sukar lamarin, gwamnan bankin ya sake gaya masa cewa ba za su cire rubutun ba.

A karshe Mai Martaba Sarkin ya yi kira ga malamai da su daina amfani da kalaman da sauran mutane suke fada musu, yana mai cewa su guji yada jita-jita, kuma su dunga yin bincike da zarar sun ji magana.

Da yake tsokaci kan batun gudar Naira 5,000, Sanusi ya ce a lokacin da yake gwamnan bankin mutane sun nuna ba daidai ba ne.

Ya ba da misali da cewa idan ka canza Dala 1200 zuwa Naira, za a ba ka Naira miliyan 1 a “Black Market”, kudin sun yi yawan da zaka sa a aljihu, sai ka dauki jaka.

Amma idan akwai gudar naira 5,000, rafa biyu kacal za a ba ku wanda ya kai miliyan 1, to za ku iya sanya kudin a aljihu ba tare da wata barazana ba.

Na tabbata nan gaba za a iya samun kudi har gudar Naira 20,000, kuma babu matsala a tattalin arziki”. Yace

Idan malamai za su yi magana a kan tattalin arziki, yana da kyau su kasance masana ko kuma su bibiyi lamarin don guje wa jefa mabiya cikin jahilci

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button